
CRYPTOCURRENCY WALLET
Tunda ka fahimci inda a ke kasuwancin cryptocurrency, sannan ka san yadda a ke yi, abu na gaba da ya rage mana shi ne mu san inda a ke adana cryptocurrency da kuma yadda a ke adanawar.
Cryptocurrency a matsayin kuɗi mai ƴanci da a ke amfani da shi wajen mu’amala ba tare da gudanarwar bankuna ba,mu’amala da su da adana su yana faruwa ne ta hanyar amfani da wallet. Hakan na nufin, wallet na ɗaukar matsayin bankuna ne a cryptocurrency, yadda za ka iya amfani
da bankuna wajen sarrafa kuɗaɗen gargajiya haka za ka iya amfani da
wallet wajen sarrafa cryptocurrencies. Wallet na da bambanci da exchanges inda a ke kasuwancin cryptocurrency, maimakon haka ana amfani da wallet ne domin; adana cryptocurrency, turawa ko kuma karɓa. Duk da ya ke, a kan samu nau’ikan wallets ɗin da su ke ba da
damar musayar cryptocurrency (converting a cikin su).
What is Wallet?
Wallet manhaja ce da a ke amfani da ita wajen adana cryptocurrency tare da sarrafa su yayin mu’amala. Ta hanyar amfani da wallet ne za ka iya adana coins naka a ciki, za ka iya turawa wani, sannan wani zai iya tura maka kamar dai yadda mu ke amfani da manhajar banki ta wayar
hannu.
How Wallet Works?
Ba kamar wallet ɗinmu ta gargajiya da mu ke iya adana tsabar kuɗaɗenmu a ciki ba, ita wallet ta cryptocurrency tana ba da adamar adana public keys da private keys ne.
● Public keys: Wannan lambobi ne da su ke ɗaukar matsayin lambobin asusu da a ke amfani da su wajen turawa ko adana
coins a cikin su. public keys na aiki ne kamar lambar asusun banki wanda idan za a turo maka kuɗi za a turo maka ne ta
cikinsu, haka idan za a turo maka cryptocurrency za a yi amfani da public keys ne a turo maka.
● Private keys: Wannan lambobin sirri ne da ke ba ka damar sarrafa asusunka na cryptocurrency, ta hanyar amfani da
su ne za ka iya tura coin ko cirewa a cikin asusunka. private keys suna aiki ne kamar lambobin sirri (Password) da a ke amfani da su domin shiga mobile bank. Adadin coin ɗin da ka mallaka suna adane a cikin blockchain, wallet naka ba damar amfani da keys ne domin sarrafa coins naka kawai. Public keys lambar asusunka ne da ke cikin blockchain wanda za a yi amfani
da shi domin turo maka coins a ciki. Private keys lambobi ne da su ke tabbatar da haƙƙin mallaka wanda idan ka sanya su za ka samu damar sarrafa coins ɗinka, idan ka rasa su kuma ka rasa coins ɗinka. Saboda haka, maimakon adana coins, wallet na ba ka damar adana keys ɗinka
ne a cikinta tare da ba ka damar sanya private keys ɗinka domin amfani da coins ɗin da ka mallaka. Misali: idan na yi amfani da wallet nawa na tura maka coins zuwa wallet naka, hakan ba ya nufin coin ɗin ya fita daga wallet ɗina ya shiga wallet ɗinka. Dama can coin ɗina ba a wallet
ɗina ya ke ba yana cikin blockchain ne, tura maka da na yi kamar nabuƙaci blockchain ne da ya ɗebe wannan adadin daga public keys ɗina ya sanya a public keys ɗinka.
Types of Cryptocurrency Wallet
Cryptocurrency wallet ta kasu izuwa manyan rukunnai gudu biyu:
1. Hot wallet
2. Cold wallet
InshaAllahu a darasin mu na gobe zamu taba bayanin kowanne daga cikin rabe raben wallet da muke dasu tare da kawo misalansu.

Leave a comment