
Asusun bankin da yafi dacewa da sana’ar crypto
A zahirin gaskiya yana da kyau wanda yake gwagwarmaya ta online bawai iya crypto ba ya tsaya ya duba bankin da zai fi dacewa da yanayin tsarin hada hadarsa. Duba da chaje chaje na ba gaira babu dalili da kowane lokaci musamman karshen kowane wata muke gani a cikin asusun bankunan mu musamman wadanda suke yawan hada hadar kudi da account, abin takaici wai idan banki zaiyi irin wannan kwashe kwashen ya tarar baka da kudi a account din sai a dora maka minus ma’ana an biyoka bashi.
To a yanzu yan crypto suna amfani da bankuna wadanda sun sabawa wanda gama garin mutane suka fi amfani dasu, wadannan bankuna suna da saurin aiki, suna da tsaro sannan kuma suna da sauki wajen chajis wasu daga cikinsu ma zaka samu basa chajis din kwata kwata sannan kuma wadannan bankunan suna bada damar kayi hada hadar kudi mai yawa a rana sabanin bankunan mu na yau da kullum da yawanci zaku ga iya miliya biyar kadai yawancinsu mutum ke da ikon turawa a kowace rana dadin dadawa bankunan mu na gargajiya zaka samu idan mutum ya samu Matsala ko yana son ayi masa gyara a account din sa sai ya shafe sati ko wata yana zirga zirga a bankin akan matsala guda daya ba tare da anyi masa maganinta ba amma su wadannan bankuna kiran waya daya na yan mintuna ya wadatar a magance maka kowace irin matsala. Wadannan sune misalai na bankunan da suka fi shahara a tsakanin yan crypto:
1. Opay bank
2. Palmpay bank
3. Kuda bank
4. Moniepoint bank
5. Chipper cash
Ba iya wadannan kadai ba, akwai ire irensu da dama da yan crypto ke amfani dasu amma wadannan sune su ka fi shahara.
Opay bank shine mafi arha ko rahusa a cikin duka bankunan dana lissafo a sama duba da cewa komai nasu kyauta ne tun daga kan transfer, maintenance, hatta ATM din su zasu baki virtual kyauta, zaki iya sayen physical kuma akan 600 maimakon 1050 da bankuna suke sayarwa. Kuma duk lokacin da zaki saka kati ta account dinki na opay zaki samu ragi akan yadda zaki saya a shago ko a sauran bankuna, misali idan zaki sayi kati na 100 zaki iya samunsa a 95, kuma zaki iya sayen unit na wuta ko bill na dstv, startimes da sauransu duka cikin rahusa.
Domin yin register da opay ki shiga wannan link din
https://mkt.opayweb.com/user-invite-friend?sceneType=general&activeType=worldCup&inviteCode=MP74b1SsprIOh5IN6il%2Ffhlnw0i9Ah%2BqMBcIx9Z1LHjw7ikiOoTNOmK4J7FcfeWU
Ko kuma ki shiga Play store kiyi download na app din opay sai kiyi register. Bayan kinyi register sai ki samu 1000 ki saka a ciki domin ki tabbatar da account dinki wadda zaki iya cirewa nan take ba tare da bata lokaci ba
Invitation code : 8069295727

Leave a comment