Tallace tallace: Abubuwan da ya kamata masu sha’awar tallata hajojinsu a group din nan su sani

Assalamu alaikum

Kamar dai yadda kowa da yake gidan nan ya kamata ya sani cewa wannan gida namu mai albarka mun budeshi ne domin samarwa yan uwa mata hanyoyin dogaro da kai a zamanance, wanda muka fi mayar da hankali akan koyar da kasuwancin Cryptocurrencies, airdrop, mining, da kuma wasu karin damarmaki da muke fatan kawo su sannu a hankali.

To a wannan karon ina yiwa masu kasuwanci na zahiri albishir da kyawawan tsaruka da kuma tanadi da mukayi musu domin bunkasa kasuwancinsu, wanda muna fatan wannan gida ya zama cibiyar kasuwanci ta mata ziryan a kafar facebook.

Sai da kuma akwai sharuda masu matukar tsauri da zamu gindaya a gidan nan ta fuskar kasuwancin wadda kuma ya zama wajibi kowacce member ta kiyaye. Domin mun tanadi hukunce hukunce masu tsauri ga duk wadda ta sabawa dokokin mu.

Kadan daga cikin dokokin sune babu gayyatar mutum ku hadu ta private ko WhatsApp, yin hakan ya sabawa dokar gidan kuma duk wadda tayi zata fuskanci dakatarwa har ta tsawon kwana 7. Sannan kuma idan kika maimaita laipin sau uku, zamu cireki daga cikin gidan baki daya. Muna so duk wata hulda ta kasuwanci a yi a cikin group kowa yana ganin abinda yake wakana, hakan zai karawa members kwarin gwiwar su saya, sannan kuma duk wacce tabi wannan dokar ta sayar da kayanta ga mutane biyu,akayi ciniki aka gama lafiya babu cuta babu cutarwa. Zamu bawa kasuwancinta gagarumar gudummawa ta hanyar mentioning din all members a kan tallarta. Na tabbatar duk yar kasuwa tasan gagarumar rawar da hakan zai taka ace yau anyi mentioning na mutum sama da dubu ashirin akan tallarki

Abu na gaba shine bamu yarda ki tura kudin ki kai tsaye ga wadda kika sayi kaya a wajenta ba, idan kinyi hakan babu wani hukunci, amma duk abinda ya biyo baya babu ruwan mu kuma ba zamu lamunci daga baya kizo kina cewa an cuce ki a group din mu ba. Duk wadanda zasuyi kasuwancinsu suyi ciniki su daidaita idan ya zama suna gari daya ko zaki iya zuwa ki karbi kayanki ki bada kudi hannu da hannu, idan kuma hakan ba zai samu ba inshaAllahu zamu ayyana wasu daga cikin mahukunta gidan nan kowace daya zatayi aiki a matsayin yar tsakiya, ma’ana idan kunyi ciniki kun daidaita kun tsayar da lokacin da za’a tura miki kaya kuma an fada miki yadda yanayin kayan yake a zahiri to zaki turawa wadannan wakilan da zamu fadi sunansu nan gaba kudin, sunan wanda kika sayi kayan a wajenta, number wayarki, inda za’a tura miki kayan da kuma screenshot na yarjejeniyar da kuka yi. Ita kuma aikinta ne tayi magana da wadda aka sayi kayan a wajenta akan ta tura miki kayanki, idan an tura miki kaya za’a baki awa 24 domin ki tabbatar da ingancin kaya idan kin samu kayan ba’a yadda aka fada miki ba za’a baki dama ki mayarwa mai kaya kayanta ke kuma a dawo miki da kudinki, idan kin samu kaya a yadda kike so to falilllahilhamdu, sai a turawa mai kaya kudinta.

Duk da dai cikakken bayani zai zo akan yadda cinikayya zata kasace a gidan nan, amma abu na karshe da zanyi magana akansa yanzu shine wajibi ne duk wacce zata tallata hajarta ya kasance an tantanceta kafin mu bata damar yin talla wannan dole ne. Dan haka idan kun bamu hadin kai munyi komai cikin tsari na tabbatar kowa zai amfana inshaAllahu.

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started