CRYPTO:DARASI NA 16

Order
A centralized exchange, mai saye ba shi da ikon sayen coin kai tsaye daga mai sayarwa sai dai ya buƙaci kasuwar ta saya masa, haka mai sayarwa ba shi da ikon sayarwa mai saye kai tsaye sai dai ya buƙaci kasuwar ta sayar masa. Nuna buƙatar a saya maka ko a sayar maka yana faruwa ne ta hanya sanya adadin coin ɗin da ka ke son saye ko sayarwa da adadin farashin da ka ke son ka sayi coin ɗin ko kuma ka sayar, wanda yin hakan shi a ke kira da “Order” Saita order hanya ce ta nunawa kasuwa buƙatar da ka ke da ita, ita kuma kasuwar sai ta aiwatar maka da buƙatar. Misali, idan ka saita order ta sayen A-coin a farashin N50, kana ba wa kasuwar umurni ne cewa ta saya maka A-coin a farashin N50. Ita kuma kasuwar za ta nemi wanda ya ke son sayar da A-coin ɗinsa a farashin da ka saita sai ta saya maka. Idan babu mai son sayar da A-coin ɗinsa a farashin da ka ke son saye
kuma, to kasuwar za ta jira har sai farashin ya sauko daidai da yadda ka saita sannan ta saya maka.

Types of Order
Order a kasuwannin cryptocurrency ta kasu kashi huɗu:
1. Market order
2. Limit order
3. Stop-loss order
4. Stop-limit order
Market Order
Market order nau’in order ce da Ɗan kasuwa zai saita domin saye ko sayar da coin ɗinsa a farashin da ya ke a kasuwa. Misali A-coin yana N50 yanzu, sai mai saye ya buƙaci sayensa a wannan farashin ko kuma mai sayarwa ya buƙaci sayar da coin ɗinsa a wannan farashin.

Limit Order
Limit order nau’in order ce da Ɗan kasuwa zai saita da niyyar sayen coin
ko sayarwa a farashin da ya ke so wanda ya bambanta da farashin da coin ɗin ya ke a kasuwa.
● Buy Limit Order: wannan nau’in order ce da Ɗan kasuwa zai saita da niyyar sayen coin a ƙasa da farashin da coin ɗin ya ke a kasuwa. Misali, A-coin yana a farashin N50 a yanzu amma Ɗan kasuwa shi a N40 ya ke son ya saye shi, sai ya saita limit orderna shi a N40 ɗin ta yadda farashin A-coin na sauka zuwa N40
kasuwar za ta saya masa ko da ba ya nan.
● Sell Limit Order: Sell limit order nau’in order ce da Ɗan kasuwa zai saita idan yana son sayar da coin ɗinsa a farashin da ya fi farashin da coin ɗin ya ke a kasuwa yanzu. Misali, A-coin yana a N40 amma Ɗan kasuwa yana son sayarwa ne a N50, sai ya saita limit order na shi a N50 ɗin ta yadda farashin na tashi zuwa haka
kasuwar za ta sayar mishi ko da ba ya nan.
Stop-Loss Order
Stop-loss order nau’in order ce da Ɗan kasuwa zai saita da niyyar idan farashin coin ɗinsa ya sauka zuwa haka to kasuwar ta sayar masa don gudun kada ya yi babbar asara. Misali, Ɗan kasuwa ya sayi A-coin a farashin N50, daga baya sai farashin ya tashi zuwa N55 kuma yana
tsoron ya sayar saboda farashin bai gama tashi ba, sai ya saita stop loss order na shi a N50 da niyyar idan farashi A-coin ya sauko yadda ya saya to a sayar mishi kawai. A wannan yanayi Ɗan kasuwar ya tsare farashin da ya saya, ko da bai ci riba ba to ba zai yi asara ba kuma.

Stop-Limit Order
Idan Ɗan kasuwa ya saita stop-limit order to ya buƙaci matuƙar farashi ya sauka zuwa kaza kuma ya sake dawowa kaza to a saya masa ko a sayar masa.

● Buy Stop-Limit Order: Ƙaddara technical analysis naka ya nuna maka cewa idan farashin A-coin ya sauko zuwa N30 to ya zo maƙurar saukarsa kenan (Support level). Amma ba ka da tabbacin lokacin da farashin zai sauko zuwa haka, sai ka saita stop price naka a N30, limit price naka a N33. Hakan na nufin ka buƙaci kasuwar ta saya maka A-coin da zarar farashinsa ya sauka zuwa N30 kuma ya sake tashi ya zo N33 to ta saya maka daidai N33 ɗin. A wannan yanayi ko da farashin A-coin ya sauka zuwa N30 ɗin da ka yi hasashen nan ne support level, kasuwar ba za ta saya maka ba sai idan farashin ya tashi zuwa N33 wanda dama haka ka yi hasashen.
● Sell Stop-Limit Order: Ƙaddara ka sayi A-coin a farashin N50 yanzu yana N55 kai kuma kana harin sayarwa a N60, to amma
ba ka da tabbacin zai kai hakan. Sai ka saita stop limit naka a N53, price limit naka kuma a N50 (farashin da ka saya). Awannan yanayi, ka buƙaci matuƙar farashin A-coin ya sauka zuwa N53 to ta sayar maka a N50 ɗin da ka saya.

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started