CRYPTO DARASI NA 14

Verification
Verification mataki ne da za a buƙaci ki sanya bayananki domin; a san ki, a gan ki sannan a tabbatar da bayanan da ki ka ba da na gaskiya ne.
Tantance ki da adana bayananki zai taimaka wajen inganta tsaron asusunki ta yadda masu kutse ba za su samu damar satar miki kuɗi ba, sannan idan wayarki ta faɗi ko kika manta password naki za a yi amfani da bayanan da ki ka bayar wajen tantance ki da sake ba ki damar sanya
wani password ɗin sabo ta yadda ba za ki yi asarar kuɗaɗenki ba.

1. Da farko zakiyi shiga app dinki na kucoin, ki saka Email da kuma password din da kika zaba yayin yin register, sai ki danna login zai kaiki inda zaki ga hoton da yake kasan nan, abinda ake so anan shine ki jawo wannan dan yanka yankan wannan guda uku zaki ga hoton samansa yana motsawa sai ki kai hoton da yake motsawa jikin dan uwanda kamar dai yadda akayi a hoto na biyu.

2. Daga nan idan wayarki tana da thumbprint zata tambayeki shin kina so ki dinga shiga app din ta hanyar amfani da thumbprint a maimakon password sai ki taba activate now kamar dai yadda yake a hoto na farko idan kin taba zai kaiki wajen hoto na biyu a nan kuma kawai zaki dora yatsan da kike bude wayarki akan thumbprint sensor kamar dai zaki bude wayar.

3. Daga nan zai nunw miki option guda biyu akwai deposit akwai ok sai ki taba ok. Zai nuna miki hoto na 2 sai ki taba alamar home wadda zaki gani da hoton gida da kima jar alamar lamba 1.

4. Idan kin taba home zai kaiki kan wanan hoton inda zaki taba wajen dana zagaye da jan layi a hoto na 1 dana 2.

Daga nan zai nuna miki inda zaki shigar da bayananki daga kasan bayanan naki zaki ga dan circle shima sai ki taba shi sannan ki taba submit.

Da zarar kinyi submit zai nuna miki cewa kin gama verification matakin farko, sai ki taba continue advance verification zai kaiki inda zaki dauki hoton id card dinki gaba da baya da kuma hoton fuskarki . Abinda zakiyi kawai shine seta id card din a cikin frame din da suka baki, daukar hoton kuma sune zasu yi.

Shikenan kin gama verification zasu fada miki ki jira na minti 5 kafin suyi approve

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started