CRYPTO: DARASI NA 13

HOW TO TRADE CRYPTOCURRENCY
Bayan munyi bayanin yadda kasuwannin cryptocurrency su ke; rabe-rabensu, bambancinsu da fa’idojin kowannen su. Abu na gaba da ya kamata mu sani shi ne yadda a ke amfani da kasuwannin wajen sayen cryptocurrency da sayarwa.
Kucoin
Kucoin na ɗaya daga cikin kasuwanni goma mafi girma, aminci, sauƙi, da shahara wanda aka fi amfani da su wajen hada-hadar cryptocurrency. An kafa ta ne a shekarar 2017. A halin yanzu, kasuwar Kucoin tana sahun gaba a cikin kasuwannin cryptocurrency da a ke amfani da su a faɗin duniya ta fuskar tara cinkoson mutane da yawan cinikin cryptocurrencies da a ke yi a
kowacce rana. Masu amfani da Kucoin sun kai kimanin; mutum miliyan 10.


How to Create Kucoin Account
Yin rijista a Kucoin ya ƙunshi bin matakai guda biyu:
1. Registration
2. Verification
Registration
Wannan mataki ne da ya shafi sanya dukkanin bayananka wanda za a
iya gane ka da su. Kafin haka, kana buƙatar sauke manjar Kucoin a Play
Store idan kana amfani da Android, ko kuma a App Store idan kana amfani da iOS ko iPadOS, masu amfani da computer kuma za su iya ziyartar website ɗin kucoin https://www.kucoin.com/r/rf/rBL9TAZ.
● Idan kina amfani da Android za ki iya yin register tare da sauke manjar kucoin
kai tsaye ta hanyar shiga wannan link ɗin
https://www.kucoin.com/r/rf/rBL9TAZ

Bayan kin shiga shafin na Kucoin, za ki bi matakan da za su biyo baya ɗaya bayan ɗaya har ki gama:
1. Bayan kin ziyarci website na Kucoin https://www.kucoin.com/r/rf/rBL9TAZ
● kina shiga zai nuna miki inda zaki saka email da kuma password, in kuma kina so ki bude da number waya sai ki taba wajen da aka saka ‘phone number’ daga saman inda zaki saka email .
● ki tabbatar passwor dinki ya hada babban baki da karamin baki sannan kuma akwai numbobi a cikinsa kamar dai yadda kuke gani a jikin hoton, bayan kin saka email kin kuma zabi password sai ki danna sign up.

2. Bayan kin taba Sign up zai dauke ki ya kai ki inda zakiyi verification da zai tabbatar musu cewa ke din mutum ce ba wai na’ura ba. Zasu baki wasu hotuna masu dauke da harafi ko lambobi daga saman hoton kuma zasu nuna miki yadda suke so ki jera, anan abinda ake so kiyi shine zaki taba hotunan ne daidai da yadda suka zo a jerin da suka bayar. A hoton da yake kasa zaku ga na zagaye muku wurin da suke nuna yadda zaku jera din.

3. Bayan kin jera hotunan da suka baki kin danna ‘OK’ Zasu tura miki verification code a Email dinki, sai kije ki duba email dinki zaki ganshi idan kin bude zaki ga numbobi guda shida sai ki kwafo su kizo wajen da suka ce ki saka verification code sai ki rubuta su, daga nan sai ki danna ‘Activate account’.

Kina gama wadannan matakan account ya budu. Zasu kai ki cikin kasuwa. Daga nan zaki iya kiyi download na app din ko daga nan inda suke nuna miki ko kuma ki shiga cikin play store.

Zaki danna wannan wajen da aka rubuta download domin sauke manhajar akan wayarki.

InshaAllahu gobe zamuyi verification kowa

Kowacce sai ta tanadi Id card nata ko voters card, national id card, ko Nin slip

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started