
Factors To Consider When Choosing Cryptocurrency Exchange
A yau, akwai kimanin fiye da cryptocurrencies exchanges guda 485 da a ke amfani da su ayi kasuwancin cryptocurrency. Galibin su ba su da nganci, akwai buƙatar yin duba na tsanaki wajen tantance exchanger kafin amfani da ita domin kiyaye kanka daga yin mummunar asara wanda zaɓar jabun kasuwa zai iya janyo maka. Akwai muhimman abubuwa guda bakwai da za ka yi la’akari da su yayin zaɓar exchanger da za ka yi amfani da ita wajen gudanar da kasuwancinka na cryptocurrency. Ga jerin abubuwan kamar haka:
1. Supported countries
2. Supported currencies
3. Liquidity
4. Transaction fees
5. Payment methods
6. Volume
7. Security
Supported Countries
Abu na farko da za ka fara bincikawa yayin zaɓar exchanger shi ne: ka duba jerin ƙasashen da a ke iya amfani da ita. Centralized exchanges ba kowacce ce ke aiki a kowacce ƙasa ba, galibin su akwai ƙasashen da ba sa aiki sakamakon rashin cika sharuɗɗan hukumomin ƙasashen. Saboda haka, ka bincika ko exchanger ɗin na aiki a ƙasarka. Za ka iya duba haka
ne ta hanyar shiga website nata.
Supported Currencies
Abu na biyu, ka duba adadin kuɗaɗen gargajiyar da a ke iya sayen
cryptocurrencies da su da kuma adadin cryptocurrencies ɗin da a ke iya
kasuwancin su a cikinta. Tunda decentralized exchanges ba sa ba da
damar amfani da kuɗaɗen gargajiya, sai ka duba adadin yawan coin ɗin
da a ke iya cinikayyar su a cikinta. Centralized exchanges ma ba kowacce
ke ba da damar amfani da kuɗaɗen gargajiya ba, ga waɗanda ke ba da
damar amfani da kuɗaɗen gargajiyar sai ka duba ko kuɗin ƙasarka na cikin jerin kuɗaɗen da a ke iya sayen cryptocurrencies da su, sannan ka
duba yawan coins ɗin da a ke iya kasuwancinsu a cikinta ko akwai irin
coin ɗin da ka ke son saye ko sayarwa a cikinta.
Liquidity
Liquidity shi ne abu na uku da za ka yi la’akari da shi. Yawan liquidity da kasuwar ke da shi zai ba ka tabbacin idan za ka sayi cryptocurrency a kasuwar za ka saya cikin sauƙi ba tare da jiran mai sayarwa ba, haka idan ka tashi sayarwa ma za ka sayar cikin sauƙi ba tare da jiran maisaye ba. Idan kasuwar babu liquidity sosai kuwa, hakan na nufin ba ta da sauƙin cinikayya sosai domin za ka iya sayen coin ka zo sayarwa babu hali sai ka jira mai saye, wataƙila kafin lokacin ma farashin coin ɗin ya sauka.
Transaction Fees
Yana da matuƙar amfani ka duba yawan cajis ɗin da kasuwar ke chaja yayin mu’amala da ita. Wasu kasuwannin suna da caji sosai da in ba adadin coin ɗin da za ka saya ko sayarwa yana da yawa ba, sai cajis ya fi kuɗin coin ɗin da za ka tura. Shi ya sa ya ke da matuƙar mahimmanci ka
duba yawan cajis da kasuwar ke caja kafin ma ka fara amfani da ita.
Payment Methods
Ga exchanges ɗin da ke ba da damar amfani da kuɗaɗen gargajiya, yana
da kyau ka duba hanyoyin biyan kuɗin da kasuwar ke aiki da su. Ka duba ko akwai wanda ka ke da shi, idan ya kasance babu wanda ka ke da shi to ba za ka iya sayen cryptocurrency da kuɗaɗenka gargajiya ba. Misali, wasu kasuwannin na aiki da; Mastercard, Visa card, PayPal, Express ko
Wire Transfer. Idan kai kuma Verve Card kaɗai ka ke da shi, ka ga ba za ka iya amfani da shi ba kenan.
Trading Volume
Trading volume na nufin adadin yawan coin ɗin da a ke hada-hadar su a kowacce rana, ko adadin kuɗaɗen da a ke hada-hadar su a kowacce rana. Yawan trading volume na kasuwa zai nuna maka yawan mutanen da ke amfani da kasuwar wajen saye da sayarwa. Yawan mutanen da ke amfani da kasuwar kuma shi zai nuna maka yadda mutane suka gamsu
da ita, gamsuwar mutane akan abu kuma shi ke nuna ingancin da abin ke da shi. Security
Abu na ƙarshe kuma mafi amfani shi ne tsaro. Cikakken tsaron da kasuwar ke da shi zai tabbatar maka da dukiyarka na cikin aminci, akasin haka kuma kana cikin yuyuwar tafka asara. Hanyoyin tsaro suna
da yawa, daga cikin abubuwan da za ka yi la’akari da su akwai:
● Two-factor authentication (2FA): makulli ne da a ke amfani da shi domin ƙara tabbatar da tsaron asusun ajiya. Bayan
password ɗinka sai a buƙaci yayin da za ka shiga asusunka ko za ka cire coins ka sanya 2FA ɗinka domin a tabbatar da kai ne ka
ke son cirewa ba masu kutse ba ne. Yana iya yuyuwa masu kutse su samu password naka su shiga asusunka da niyyar ɗebe maka coins, domin hana faruwar hakan sai kasuwanni ke amfani da 2FA ta hanyar tura maka lambobi guda shida a lambar wayarka, kai kuma sai ka sanya lambobin a kasuwar kafin a ba ka damar
cirewa. Wasu kasuwannin kuma suna amfani da guda biyu; 2FA na lambar waya da kuma na Authenticator. Dabarar amfani da 2FA shi ne, a nunawa ɓarawo idan ya iya ruwa ai bai iya laka ba, idan zai iya samun password naka ya shiga account naka ai ba zai iya kuma ɗauke wayarka ba, idan kuma ya san password
naka kuma ya ɗauke wayarka to ka binciki na kusa da kai. Saboda haka, ka duba ko kasuwar nada 2FA, idan ba ta da shi
kamar gida ne wanda ke da ƙofa babu mai gadi, ka ga tsaron gidan ba shi da ƙarfi sosai.
● Cold storage: Wannan rumbun adana cryptocurrency ne da ba ya kan internet wanda centralized exchanges ke adana coins ɗin masu amfani da su a ciki domin kaucewa haɗarin masu kutse. Masu kutse suna iya yiwa exchanges kutse ne idan tana adana coins ɗin mutane a rumbunta da ke kan internet (Hot storage). Saboda haka, ka duba ka ga ko kasuwar nada cold storage, idanba ta da shi ka sanya a ranka cewa ko da yaushe masu kutse suna
iya yi mata kutse.
InshaAllahu gobe da misalin karfe 10 na safe zamu tatauna akan darussa goma sha biyu da suka gabata, kafin mu shiga darasin mu na gaba wato
‘HOW TO TRADE CRYPTOCURRENCY’ Ma’ana yadda mutum zaiyi cinikayyar kudaden Internet.

Leave a comment