
Hybrids Exchanges (HEX)
Hybrid exchanges kasuwanni cryptocurrency ne da suka haɗa ayyuka
da tsarukan centralized exchanges da decentralised exchanges a guri ɗaya. Dabarar samar da irin waɗannan kasuwannin shi ne: domin a
kawar da raunin da ke tattare da centralised da decentralized exchanges
ta yadda Ɗan kasuwa zai mori fa’idodin da ke cikin kasuwannin biyu a guri ɗaya. Ta fuskar samar da kyakkyawan tsarin gudanar da kasuwancin cryptocurrency centralized sun fi decentralised exchanges, ta fuskar samar da tsaro da ba da cikakken ƴancin cinikayya ba tare dashinge ba kuma decentralised exchanges sun fi centralized exchanges. Saboda haka ne aka samar da hybrid exchanges da niyyar amfani da kyakkyawan tsarin gudanarwa da ke cikin centralized da kuma cikakken tsaron adana bayanai da ba wa Ƴan kasuwa cikakken ƴanci da ke a decentralised exchange. Hybrid exchanges na ƙunshe da fa’idodin da ke a cikin kasuwannin guda biyu, sannan ta kawar da raunin da ke cikin kasuwannin domin samar da kasuwa ɗaya mai tarin fa’idodi da rashin matsaloli.
Hybrid exchanges su ne nau’inkan kasuwanni crypto sabon yayi da za a
yi amfani da su a nan gaba. A halin yanzu, babu nau’ikan hybrid exchanges da suka fara aiki gadan-gadan, amma akwai da dama waɗanda a ke kan samarwa, daga cikinsu akwai waɗanda suna kan
matakin ƙarshe na fara aiki yayin da wasu ke kan matakin gwaji kamar
http://www.qurrex.com http://www.espay.exchange da sauransu.
InshaAllahu gobe zamuyi bayani akan abubuwan da ake dubawa domin zaben kasuwar da zaka ji dadin kasuwanci da ita.

Leave a comment