CRYPTO: DARASI NA 10

Pros And Cons of Decentralized Exchanges
Decentralized exchanges na da tarin fa’idodin da za su sanya a buƙaci amfani da su, a wani ɓangaren kuma suna da matsalolin da zai sa a ƙi amfani da su.

Pros
✓ Anonymity
✓ Global accessibility
✓ Difficult to hack
✓ Low fees
✓ Non-custodial
✓ More trading options
Anonymity
Yayin amfani da decentralized exchanges ba a buƙatar yin rijista ko buɗe asusun ajiya ballantana a samu bayananka da za a iya amfani da su a gane ka ko a gane inda ka ke. Idan ko ya kasance za ka iya sayen cryptocurrency ko ka sayar ba tare da an iya gane ka ba, hakan na nuna ba za a iya sanin mai ka saya, mai ka sayar, adadin da ka saya da kuma adadin da ka sayar ba. Ba kamar centralized exchanges da kafin amfani da su sai an yi rijista kuma sai an tantance bayanan da aka bayar ba.
Global Accessibility
Yana daga cikin fa’idodin amfani da decentralized exchanges shi ne, za
ka iya sayen cryptocurrency ko ka sayar a kowacce ƙasa ka ke a faɗin duniya ko da kuwa a ƙasar an haramta kasuwancin cryptocurrency. Kasuwannin sun dogara ne kacokan da blockchain, saye da sayarwar da a ke yi a cikinsu yana gudana ne da taimakon smart contract. Saboda
haka, ba za a iya hana mutanen wata ƙasar shiga cikin kasuwannin ba, idan ko ana so a hana to sai dai a hana amfani da internet a ƙasar gaba ɗaya, amma matuƙar akwai internet to babu shakka mutane za su iya saye da sayarwa a decentralised exchanges.
Difficult To Hack
Kasancewar decentralised exchanges sun dogara ne da blockchain wajen tattara bayanai, blockchain kuwa na amfani ne da distributed leader da ke rarraba bayanan mu’amaloli ga computers da wayoyin da
a ke amfani da su a yi mu’amala akan wannan blockchain ɗin, masu kutse ba za su iya yiwa kasuwannin kutse a cikin sauƙi ba. Kafin su samu damar yiwa kasuwar kutse sai idan za su iya tattaro wayoyi da
computers ɗin da a ke amfani da su a shiga kasuwar, wanda hakan kuma ba abu ne mai yuyuwa ba. Sannan ko da ma masu kutsen sun samu damar yiwa kasuwar kutse, kasancewar masu amfani da kasuwannin ba sa ajiye coins ɗinsu a ciki to ba za su yi asarar komai ba.

Low Fees
Wani abin ƙayatarwa da irin waɗannan kasuwannin shi ne cajis ɗin da
su ke chajar masu mu’amala da su kaɗan ne duk da ya ke ya ta’allaka ne da blockchain ɗin da kasuwar ke aiki da shi. Irin su PancakeSwap, Sushiswap, 1Inch da su ke akan Binance smart-chain suna da sauƙin cajis sosai idan aka kwatanta su da nau’ikan centralized exchanges irin
su Binance, Coinbase da sauransu.
Non-custodial
Yayin amfani da decentralized exchanges ba a buɗe asusun ajiya a kasuwar ballantana ya zama dole sai an ajiye coins a ciki kafin a iya saye ko sayarwa. Wallet kawai za a jona a sayar da coins nan take kuɗin da aka sayar su shiga wallet na mai sayarwa, ba kamar centralized exchanges da dole sai an ajiye coins a cikinsu kafin a iya sayarwa ba.
More Trading Options
Decentralized exchanges na ɗauke da dubannin cryptocurrencies kala- kala, kusan duk cryptocurrency ɗin da za a buƙaci saye ko sayarwa akwai a cikinsu sakamakon ƙaddamar da sabbin cryptocurrencies a cikinsu babu wahalarwa ta yadda hatta waɗanda ba su iya cika sharaɗoɗin ƙaddamarwa a centralized exchanges ba suna samun damar ƙaddamarwa a nan.
Cons
● No fiat-to-crypto
● Not user-friendly
● No recovery
● Not reliable
● Low liquidity

No Fiat-to-Crypto
Decentralized exchange ba sa ba da damar sayen cryptocurrency ko sayarwa da kuɗaɗen gargajiya. Idan kana buƙatar sayen cryptocurrency a matakin farko dole sai dai ka yi amfani da centralised exchanges, sakamakon a decentralised exchanges musayar cryptocurrencies a ke,
ma’ana ka ba da wani cryptocurrency ka karɓi wani cryptocurrency ɗin daban. Sabon shiga ba zai samu damar sayen cryptocurrency da kuɗaɗensa na banki ba, sannan ba zai samu damar sayar da
cryptocurrency a biya shi da kuɗaɗen banki ba.
Not User-Friendly
Decentralized exchange ba su da fasali mai sauƙin fahimta da ake warewa musamman domin masu koyo, ƙwararru da masu koyon duka fasali ɗaya su ke amfani da shi. A sakamakon haka, amfani da irin waɗannan kasuwa yana gagarar masu koyo har sai sun ɗauki lokacin
mai ɗan tsayi kafin su iya amfani da su daidai.
No Recovery
Idan wani abu ya faru yayin amfani da decentralized exchanges kuma ya janyo maka asara to babu yadda za ka yi ka dawo da abin da ka rasa sai dai ka ɗaga hannu ka ɗora a kai ko kuma kai ta sallallami, amma asara kam ka riga ka yi. Saboda haka, akwai buƙatar sanya hankali da natsuwa sosai yayin amfani da su.
Not Reliable
Decentralized exchanges tamkar bariki su ke: uwa ba kwaɓa uba babu ƙwaba, duk mu’amalolin da a ke yi a cikinsu babu mai kula da tantancewa. Abu mai sauƙi ne ka sayi jabun cryptocurrency a cikinsu
saboda rashin tsarin tantance inganci kafin saka coin, sannan kowa mana iya saka cryptocurrency kuma ya sayar ko da jabu ne mara ingancinci.
Slippage
Slippage na faruwa ne idan mai sayar da coin ya sanyawa coin ɗin
farashin da ya wuce farashin da a ke sayar da shi a kasuwa a daidai wannan lokacin. A decentralised exchanges galibi a kan samu coins da dama wanda su ke da slippage, idan za ka saye su farashinsu daban idan za ka sayar farashinsu daban, ana zuƙa farashi idan za ka saya sannan
ana rage farashi idan za ka sayar. Amma wannan na faruwa ga iya wasu coin ɗin kaɗai, yayin da yawan coins kuma ba su da shi ma.
Low Liquidity
Liquidity yana yin ƙaranci a decentralised exchanges ta yadda cryptocurrencies da dama idan ka saye su ba za ka iya sayar ba, wani lokacin ma ba za ka iya sayen su ba ko kuma ba za ka iya sayen adadin da ka ke so ba. Wani lokacin kuma idan za ka sayi cryptocurrency a cikin adadin da za ka saya sai an ɗauki wani adadi an sanya a cikin liquidity, haka ma idan za ka sayar.

inshaAllahu gobe zamu takaita bayani akan Hybrids Exchanges (HEX)

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started