Decentralized Exchange (DEX)

Decentralised exchanges nau’ikan kasuwannin cryptocurrency ne da ke
ba wa Ƴan kasuwa damar su yi cinikayya a tsakaninsu ba tare da sa hannun hukumomin kasuwar ba. Hakan na nufin; mai saye zai sayicryptocurrency ɗin da ya ke so kai tsaye daga mai sayarwa, mai sayarwa zai sayar da cryptocurrency ɗinsa kai tsaye ga mai saye ba tare da
hukumomin kasuwar sun shiga tsakaninsu domin sasantawa ko tantancewa ba. Irin waɗannan nau’ikan kasuwannin sun fi kama da kasuwanninmu na zahiri inda mai saye ke shiga ya ga kayan da ya ke so kuma ya saya a gurin mai sayarwa kai tsaye.
A ‘Centralized exchanges’ hada-hadar cryptocurrency a cikinsu yana faruwa ne tsakanin mutane uku; mai saye, mai sayarwa da kuma kasuwar. Mai saye ba ya sayen cryptocurrency kai tsaye daga mai
sayarwa sai dai ya buƙaci kasuwar ta saya masa, mai sayarwa ba ya sayar da cryptocurrency ɗinsa kai tsaye ga mai buƙatar saye sai dai ya buƙaci kasuwar ta sayar masa. Amma a decentralised exchanges mai saye da mai sayarwa ne su ke cinikayya a tsakaninsu, mai saye ya saya kuma ya biya mai sayarwa kuɗin cryptocurrency ɗin da ya saya, sannan
mai sayarwa ya ba wa mai saye adadin cryptocurrency ɗin da ya sayar masa.
Best Decentralized Exchanges In 2021
Daga cikin nau’ikan decentralized exchanges da suka fi shahara kuma aka fi amfani da su akwai:
1. Uniswap (V3)
2. PancakeSwap (V2)
3. dYdX
4. ApolloX DEX
5. Deri Protocol
6. TraderJoe
7. Biswap
8. Curve Finance
9. SpookySwap
10. Kine Protocol
11. 1inch Exchange
12. Honeyswap
13. Sushiswap
14. Quickswap
15. Raydium
16. Serum DEX
17. SpiritSwap
18. Terraswap
19. Perpetual Protocol
20. Pangolin
How Decentralized Exchanges Works?
Kasancewar mutane na saye da sayarwa ne a decentralized exchanges ba a ƙarƙashin gudanarwar hukumomin kasuwannin, mai karatu zai so ya san yadda mutanen da ke zaune a ƙasashe daban-daban za su iya haɗuwa a wata kasuwa su yi kasuwanci ba tare da kasuwar na sanya ido akansu ba, kuma ya kasance an yi an gama ba tare da wani ya cuci wani ba. Decentralised exchanges na aiki ne ta hanyar amfani da tsaruka kamar haka:
No Sign up & KYC
Decentralized exchanges ba su da tsarin yin rijista ko buɗe asusun ajiya, suna ba wa mutane damar amfani da su ba tare da sun yi rijista ko sun buɗe asusun ajiya ba. Kamar kasuwanninmu ne na zahiri, inda za ka iya shiga ka yi sayayya ba tare da ka yi rijista ba domin babu wata hukuma a kasuwar da ke kula ko tantance masu saye da sayarwa.
Connect Your Wallet
Decentralized exchanges ba su da tsarin buɗe asusun ajiya wanda mai saye zai ajiye kuɗinsa a ciki mai sayarwa kuma ya ajiye abin da zai sayar a ciki, maimakon haka kowa zai yi amfani da wallet ɗinsa ta musamman ne da ya ke da ita. Kasuwannin da kamfanonin da su ke samar da wallet suna ba wa masu sayayya damar jona wallet nasu da kasuwar. Hakan na nufin, abin da za ka yi amfani da shi a matsayin kuɗin sayayya da kuma cryptocurrency ɗin da ka ke son sayarwa duka za ka ajiye su a cikin wallet ɗinka ta musamman ne, idan ka shiga kasuwar sai ka jona wallet ɗin da kasuwar. Kamar dai yadda ya ke idan za ka je sayayya a wani shago da ke a kasuwanninmu na zahiri, za ka ta fi da kuɗinka ne a aljihunka sannan shi kuma mai shagon zai ajiye kayan da ya ke sayarwar a shagon, idan ka saya ka biya sai a ba ka kayan ka tafi.
Place An Order
Bayan ka jona wallet naka da kasuwar, abu na gaba da za ka yi shi ne za ka zaɓi abin da ka ke son saye ko sayarwa, ka sanya adadin da ka ke son saye ko sayarwar sannan ka danna alamar saye ko sayarwa. Kamar yadda ya ke a zahiri, idan ka je shago za ka nuna abin da ka ke so ne kuma ka faɗi adadin da ka ke so, kai kuma a faɗa maka kuɗin ka biya.
Smart Contract Automates Trading
Bayan ka zaɓi abin da ka ke so kuma ka danna alamar buƙatar saye, abu na ƙarshe shi ne a zare jumillar kuɗin cryptocurrency ɗin da ka saya daga wallet naka sannan a sanya maka cryptocurrency ɗin da ka saya a cikin wallet naka, hakan na faruwa ne da taimakon tsarin smart contract.
Smart contract: tsari ne da a ke amfani da shi wajen ƙulla yarjejeniya.
Da zarar aka ƙulla yarjejeniyar sai smart contract ya tabbatar da abin da aka
ƙulla ɗin nan an aiwatar da shi daidai.
Yayin da ka sanya adadin coin ɗin da za ka saya kuma aka nuna maka jumillar kuɗin da za ka biya sannan ka danna alamar amincewa, to kamar ka ƙulla yarjejeniya da mai sayarwa ne, saboda haka smart
contract zai tabbatar da jumillar kuɗin cryptocurrency ɗin da ka saya ya fita daga wallet naka, sannan adadin cryptocurrency ɗin da ka saya kuma ya shiga wallet naka. Kai mai saye abin da ka saya ba zai taɓa shiga wallet naka ba sai idan adadin kuɗin da za ka biya sun fice daga wallet naka, mai sayarwa ma kuɗin kayansa ba za su taɓa shiga wallet na shi ba sai kayan da ya sayar sun fita daga wallet na shi. Ta haka ne smart contract ya ke taimakawa ayi kasuwancin ba tare da wani ya zalunci wani ba.
Gobe inshaAllahu zamuyi bayani akan muhimmanci da matsalolin Decentralized exchanges.

Leave a comment