CRYPTO: DARASI NA 8

Pros And Cons of Centralized Exchanges

Centralized exchanges suna tattare da fa’idodi da yawa, a wani ɓangaren kuma suna ɗauke da matsaloli da yawa wanda amfani da su kan iya haifarwa.


Pros / Alfanu / amfani


✓ User-friendly
✓ Customer service
✓ Reliable
✓ Fiat-to-crypto✓ Recovery possible
✓ Multiple payment methods
✓ Trading styles

User-Friendly
Centralized exchanges an tsara su ta sigar da za su yi sauƙin fahimta ta yadda hatta mai koyo zai iya fahimtar yadda a ke saye da sayarwa a cikin sauƙi. Galibin kasuwannin suna da fasalin ‘Lite’ da ‘Pro’.


Lite: yanayi ne mai sauƙin fahimta da aka samar musamman domin masu koyo.
Idan ka saita ‘Lite’ za ka ga an taiƙaita komai ta yadda ba za ka sha wahalar
fahimtar yadda a ke amfani da kasuwar ba.
Pro: yanayi ne mai rikitarwa da aka samar musamman domin waɗanda suka ƙware sosai. Pro na ɗauke da abubuwan da yawanci ba sa bayyana a Lite.

Customer Service
Centralized exchanges na samar da tsarin zantawa da wakilansu domin yin tambaya ko yin ƙorafi idan buƙatar hakan ta taso. Idan kana fuskantar wata matsala yayin amfani da su ko kana son yin tambaya
akan wani tsari da ba ka gane ba kana iya tuntuɓar su kai tsaye kuma su saurare ka.

Reliable
Amfanin da centralised exchanges wajen sayen cryptocurrency ya fi aminci da salama kasancewar suna da tsarin tantance masu saye da masu sayarwa, sannan suna shiga tsakani domin su tabbatar an gudanar da cinikayya a sigar da babu cuta babu cutarwa.

Fiat-to-Crypto
Wasu daga cikin nau’ikan centralized exchanges na ba da damar a sayi
cryptocurrency ta hanyar amfani da kuɗaɗen gargajiya ta yadda mai saye zai iya amfani da kuɗaɗensa na banki ya sayi coin, haka ma mai sayarwa zai iya sayar da cryptocurrency a sanya masa kuɗin a asusunsa na banki.

Recovery Possible
Kasancewar kafin fara amfani da centralised exchange dole sai ka yi rijistar buɗewa wanda za a buƙaci bayananka kuma sai an tantance bayanan kafin a ba ka damar fara saye ko sayarwa, hakan na taimakawa yayin da ka manta password naka za ka iya dawo da shi. Idan ka ajiye
coins naka a cikin waɗannan kasuwanin to ko da ka manta password naka to ba ka yi asarar kuɗaɗenka ba, domin za ka iya buƙatar canja password sai kasuwar ta yi amfani da bayanan da ka bayar lokacin
rijista, a tambaye ka su idan ka iya tabbatar da kanka sai a ba ka damar canja sabon password.

Multiple Payment Methods
Da ya ke mutane daga sassa daban-daban na faɗin duniya ne ke tattaruwa a centralized exchanges domin gudanar da kasuwancin cryptocurrency, kasuwannin suna samar da hanyoyin biyan kuɗaɗe
daban-daban da ako wacce ƙasa ka ke za ka iya amfani da irin hanyar biyan kuɗin da ku ke amfani da shi a ƙasarku ka sayi cryptocurrency ko ka sayar a biya ka.

Trading Styles
Centralized exchanges suna ba da damar gudanar da salon kasuwancin cryptocurrency daban-daban ta yadda Ɗan kasuwa zai zaɓi salon da ya fi ƙayatar da shi ya ke amfani da shi.

Cons / Matsala / Rashin amfani


● No anonymity
● Higher risk of hacking attacks
● Price manipulation
● Custodial
● Not global accessible
● Transaction limitations

No Anonymity
Yayin amfani da centralised exchanges dole sai ka yi rijista wanda sai ka sanya cikakken bayananka, saboda haka duk mu’amalolin da ka ke yi a cikin kasuwannin ana iya gani kuma a gane ka. Sannan kasuwar tana iya
sanin daga ƙasar da ka ke ta yadda idan ƙasarka ta hana amfani da cryptocurrency kasuwar za ta iya hana ka saye ko sayarwa.

Higher Risk of Hacking Attacks Saboda kuɗaɗe da bayanan masu hada-hada a kasuwannin yana tattare a rumbun ajiyar bayanai na kasuwar, hakan wata dama ce ga masu yin kutse su iya gane inda za su kai hari kai tsaye. Shi ya sa mafi yawan irin waɗannan nau’ikan kasuwannin an taɓa yi masu kutse an saci maƙudan kuɗaɗe a cikinsu, duk da asarar bata cika shafar masu ajiyar kuɗaɗensu a kasuwanni ba.

Price Manipulation
Centralized exchanges an sha zarginsu da ha’intar farashin cryptocurrencies musamman yayin ƙaddamar da sabbin
cryptocurrencies a kasuwannin ta hanyar ɗaga farashin coin sai mutane da yawa sun saya sai su mayar da farashin yadda ya ke, hakan kuma na janyowa mutane asara sosai.

Custodial
Yayin amfani da centralised exchanges dole sai Ɗan kasuwa ya buɗe asusun ajiya wanda zai sanya kuɗin da zai sayi cryptocurrency da su ko ajiye cryptocurrency ɗin da ya ke son sayarwa. A sakamakon haka, Ɗan kasuwa ba shi da cikakken ikon sarrafa dukiyarsa sai yadda kasuwar ta tsara masa, wani lokacin ma kasuwannin suna iya hana cire kuɗi musamman idan suna yin gyara. Wata buƙata ta musamman za ta iya tasowa ka buƙaci amfani da kuɗaɗenka amma ka tarar an hana cirewa a lokacin.

Not Global Accessible
Ba a kowacce ƙasa za ka iya sayen cryptocurrency a cikin centralized
exchanges ba sakamakon sai an yi rijista a ke amfani da su, sannan suna amfani da database ne wajen adana bayanai maimakon amfani da distributed ledger. Saboda haka, mutanen da ke a ƙasashen da aka haramta kasuwancin cryptocurrency ba za su samu damar shiga kasuwanni ba.

Transaction Limitation
Kasancewar centralized exchanges cibiyoyi ne da ke aiki kamar banki, masu amfani da su ba kowanne adadin coin za su iya ajiyewa, cirewa ko turawa ba. Suna da ƙayyadadden adadin da su ke ba da damar sanyawa, cirewa ko turawa a kowacce rana. Idan ka cinye wannan adadin sai dai
ka jira zuwa gobe kafin ka iya amfani da wani adadin.

Jiya munyi bayani akan daya daga cikin Cryptocurrency exchanges da muke da su wato centralized exchanges, yau munyi bayani akan amfani darashin amfaninta, inshaAllahu gobe zamuyi bayani akan Decentralized exchanges.

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started