CRYPTO: DARASI NA 7

What Are Cryptocurrency Exchanges?

Cryptocurrency exchanges kasuwanni ne da ke wanzuwa akan internet wanda ke ba wa mutane daga sassa daban-daban na faɗin duniya damar; sayen cryptocurrency, sayar da cryptocurrency, musayar cryptocurrency ko kuma adana cryptocurrency a cikinsu. Aikin waɗannan kasuwanni shi ne: su samar da yanayi wanda zai ba wa mai buƙatar sayen cryptocurrency daga ko ina ya ke a faɗin duniya damar da zai ga kalar cryptocurrency ɗin da ya ke son saye kuma ya saya ba tare da wata matsala ba. Bugu da ƙari, ayyukan kasuwannin sun haɗa da:

● Samar da rumbun ajiyar bayanai (Database) domin adana bayanan dukkanin hada-hadar da a ke yi a cikinsu ta yadda masu saye da masu sayarwa za su iya bincikawa su ga bayanan; cryptocurrencies ɗin da suka saya ko suka sayar, lokacin dasuka saya ko suka sayar, farashin da suka saya ko suka sayar da dukkanin bayanin abin da suka gudanar a cikinsu.

● Samar da ingantaccen tsaro don ƙare dukiyoyin masu saye da masu sayarwa ta yadda wani ba zai cuci wani ba a tsakaninsu, ta yadda mai saye zai samu abin da ya saya sannan mai sayarwa ma zai karɓi kuɗin abin da ya sayar cikin aminci da salama.

● Samar da dokoki da tsare-tsare masu kyau da za a gudanar da kasuwancin akansu domin samar da aminci da biyan buƙatun masu saye da masu sayarwa.

● Samar da hanyoyin biyan kuɗaɗe daban-daban saboda mutane daban-daban da ke zaune a gurare daban-daban ta yadda za su iya sayen cryptocurrency daban-daban kuma su biya a duk inda su ke a faɗin duniya.

● Samar da guraren ajiyar cryptocurrency ta yadda Ƴan kasuwa za su iya adana kuɗaɗensu ko cryptocurrencies ɗinsu idan ba sa buƙatar saye ko sayarwa a lokacin.

Types of cryptocurrency exchanges

Kasuwannin hada-hadar cryptocurrency sun kasu kashi uku:
❖ Centralized exchanges (CEX)
❖ Decentralised exchanges (DEX)
❖ Hybrid exchanges (HEX)

Centralized Exchanges (CEX)
Centralized exchanges nau’ikan kasuwannin cryptocurrency ne wanda a ke saye ko sayar da cryptocurrency a cikinsu bisa tsari da jagorancin hukumomin kasuwannin. Hakan na nufin, hukumomin ne ke kula da duk mu’amalolin da a ke yi a kasuwannin ta hanyar samar da dokokin yadda za a gudanar da kasuwancin, kula da tantance masu saye da sayarwa, saya wa wanda ke son saye da sayar wa wanda ke son ya sayar da cryptocurrency ɗinsa. Za a iya kiran waɗannan nau’ikan kasuwannin da “Kasuwannin dillancin cryptocurrency” mai ya sa na ce za a iya alaƙanta kalmar ‘Dillanci’ a cikinsu? Saboda aikin dillali shi ne ya haɗa mai saye da mai sayarwa kuma ya sasanta su tare da sama masu tsarin da za su yi cinikayyar cikin aminci. Dillali shi ne mutumin tsakiya (Middle man) wanda ke a tsakanin mai saye da mai sayarwa ta yadda idan kana son sayar da wani abu dillali zaka ba wa talla, sannan idan kana son sayen wani abu nan ma dillali za ka ba wa cigiyar neman mai buƙatar sayarwa. Kamar haka centralized exchanges su ke aiki: idan kana son sayen coin cikinsu za ka shiga su haɗa ka da mai sayarwa, idan za ka biya kuɗin coin ɗin da ka saya su za ka ba wa su kuma su ba wa mai sayarwa, idan mai sayarwa zai ba ka coin ɗin da ka sayar su zai ba wa su kuma su ba ka.
Centralized exchanges suna kuma da kamanceceniya da bankuna ta fuskar ikon kula da duk cinikayyar da a ke yi a cikinsu kamar yadda bankuna ke kula da duk mu’amalolin da a ke yi a cikinsu. Yadda a ke gudanar da kasuwancin cryptocurrency a cikin centralised exchanges ya yi kama da yadda a ke yin mu’amalolin kuɗi a bankuna ne ta abubuwa kamar haka:

❖ Kafin ka fara aiki da kasuwannin sai ka buɗe asusu a cikinsu, yayin buɗewa za a buƙaci bayananka harda katin shaidarka
kamar dai yadda bankuna su ke.

❖ Za ka sanya kuɗaɗenka a asusunka na kasuwar ka ajiye a ciki kamar yadda a ke sanya kuɗi a asusun banki.

❖ Za ka bincika cryptocurrency ɗin da ka ke son saye, kowanne cryptocurrency za ka gansa da farashinsa ya danganta da ƙasar da ka ke, idan kana Nijeriya ne za ka ga farashin kowanne coin da Naira.

❖ Za ka zaɓi cryptocurrency ɗin da ka ke son saye, kasuwar za ta nuna maka masu son sayarwa, za ka buƙaci saye akan wani
adadin farashi, kasuwar za ta bincika wanda ke son sayar da coin ɗinsa a farashin da ka saita.
❖ Kasuwar za ta cire kuɗaɗe daga asusunka gwargwadon adadin  cryptocurrency ɗin da ka saya sai ta sanya a asusun wanda ya sayar maka sannan ta cire adadin da ka saya daga asusun mai
sayarwa ta sanya maka a naka asusun. Kamar dai yadda bankuna ke cire kuɗi daga asusunka su sanya a asusun wanda
ka turawa. Sannan za a iya fassara centralized exchange da “Cibiyar musayar
cryptocurrency” domin mutane daga sassa daban-daban na faɗin duniya ke shiga cikinsu su sayi cryptocurrency ko su sayar ƙarƙashin jagorancin hukumomin kasuwar.

Best Centralized Exchanges In 2022
Akwai nau’inkan centralized exchanges da yawa, daga cikin waɗanda suka fi shahara kuma aka fi saye da sayarwar cryptocurrency a cikinsu akwai:
1. Binance
2. Coinbase
3. FTX
4. Kraken
5. Crypto.com
6. KuCoin
7. Huobi Global
8. Gate.io
9. Bitfinex
10. Gemini
11. Binance.us
12. Bitstamp
13. Bybit
14. FTX US
15. bitFlyer
16. Coincheck
17. Bithumb
18. OKEx
19. Poloniex
20. Coinone

InshaAllahu gobe zamu yi bayanin amfani darashin amfanin Centralized exchangers.

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started