Matsalolin amfani da VPN
Da farko ma’anar vpn shine virtual private network wanda asalin aikinsa shine samar da tsaro ga na’ura tare da boye IP address naka. Wanda hakan zai baka damar shiga shafukan yanar gizo wanda aka haramta maka ko aka haramtawa yan kasar daka fito amfani dasu. Misali duk wanda yasan lokacin da aka rufe Twitter a Nigeria ta yadda duk wani mutum da yake cikin Nigeria bazai iya amfani da ita ba, amma ta hanyar amfani da VPN zaka iya mayar da location din ka ya koma wata kasa daban kamar America, England, Saudi Arabia da dai sauransu har ka iya amfani da Twitter.
Stark VPN suna boye bayanan hada hadarka ta yanar gizo ba tare da ISP (Internet Service Providers) ma’ana layukan da suke sadaka da yanar gizo sun iya bibiya ba ta yadda ba zasu iya chajarka ba.
Mutanen da bai kamata suyi amfani da VPN na stark ba sun hada da;
1. Masu hada hadar Crypto currency
2. Masu yawan ta’ammali na kudi a cikin wayoyinsu (wadanda suke amfani da mobile app na banki da wayoyinsu kuma suna turawa da karbar kudi a kai akai).
3. Masu ajiye hotuna ko bidiyoyin sirri a cikin wayoyinsu, kuma koda kuwa sun boye su a cikin vault, Ko wasu bayanai na sirri.
Dukkanin wadannan suna bukatar sirri duba da matukar hadarin da suke dashi, wanda matukar mutum yana ta’ammali dasu bai kamata yayi amfani da VPN stark ba ko duk wani VPN na kyauta ba domin zasu iya daukar bayananka har suyi maka kutse wanda hakan zai iya janyo asarar dukiya ko mutunci.
Da yawa mutane kan ajiye wasu bayanai nasu na sirri a cikin wayoyinsu amma sai kayi mamakin yadda suka fito duniya ta gani, hakan na faruwa ne ta dalilin amfani da ire iren wadannan app din zasu dauki bayananka suyi amfani da wanda zasu yi musu amfani su kuma sayar da sauran. Misali idan sun dauki bayananka na banki zasu iya yi maka sata, haka kuma idan ke ma’abociyar ajiye hotuna ko videon tsiraicinki ko na kawayenki ko video na wasu ma’amuloli tsakaninki da saurayinki ko mijinki zasu iya sayar da wadannan bayanai ga shafukan batsa wanda su kuma zasu dora a shafukansu duk duniya kowa ya gani.


Leave a comment