Stablecoins
Stablecoins nau’inkan cryptocurrency ne da a ke samar da su
musamman domin su wakilci darajar kuɗaɗen zahiri ko kuma wata
kadara da ta ke a zahiri. Misali: USDT, BUSD, TUSD da aka samar domin
su wakilci darajar Dollar America a duniyar cryptocurrency. Waɗannan
nau’inkan coins ɗin suna ta shi ne kawai idan darajar Dollar America ta
tashi, suna sauka ne kawai idan darajar Dollar America ta sauka. Ana
ƙirƙirar su ne da tsarin da ba za su wuce Dollar America ba, sannan ba
za su gaza Dollar America ba (1 USDT= $1). Suna aiki ne kamar yadda
stabilizer ke aiki a wutar lantarki: idan wuta ta yi yawa sai stabilizer ta
rage wutar, idan wuta ta yi kaɗan kuma sai ta ƙara wutar ta yadda ba za ta yi kaɗan ba sannan ba za ta yi yawa ba. Kamar haka stablecoin su ke,
idan Dollar America ta tashi sai su ma su tashi, idan ta sauka sai su masu sauka, a kowane lokaci dai darajarsu za ta daidaita ne da darajar
Dollar America.
Stablecoins suna iya daukar darajar wata kadara ta zahiri ta yadda
farashinsu a ko da yaushe zai daidaita da farashin kadarar a kasuwa.
Misali, stablecoin na zinare farashinsa ko da yaushe zai dinga zama ne a farashin da zinare ya ke a kasuwa. Idan zinare a kasuwa yana N100 to
shi ma coin ɗin farashinsa zai tsaya a N100 ta yadda ba zai wuce farashin
zinarin ko ya gaza ba.
Dabarar samar da irin waɗannan cryptocurrencies ɗin shi ne: idan kana
son sayen wata kadara da ta ke a zahiri domin ka sayar da ita wata rana,
maimakon ka sayi kadarar sai ka nemi stablecoin da ke wakiltar kadarar
ka saya, duk lokacin da ka ke son sayarwa to farashinsa dai ba zai yi ƙasa
da farashin kadarar ba. Sannan stablecoin ɗin da su ke wakiltar Dollar
America ko wani kuɗin daban, amfaninsu shi ne: maimakon ka ajiye
Dollar a asusun bankinka sai ka ajiye su a wallet naka. Akwai mutanen
da sun yarda da cryptocurrency kuma sun fahimci fa’idar amfani da
cryptocurrency, amma ba sa son sayen coins don gudun kada su saya
farashin coin ɗin ya sauka su yi asara, sai su ke sayen stablecoins tunda
su farashinsu ba ya yin ƙasa da kuɗin da su ke wakilta. Ƴan crypto kuma
suna amfani da stablecoin ne a matsayin jarin yin kasuwancinsu, idan
sun ga coin ɗin da za su saya sai su saya da stablecoin ɗin da su ke da
shi, idan za su sayar da coin ɗin sai su sayar a ba su stablecoin.
Stablecoins sun bambanta da sauran cryptocurrencies wajen zuwa da
ƙayyadadden adadi, su ba su da takamaiman adadi; adadinsu na iya
ƙaruwa kuma yana iya raguwa a ko da yaushe.
Central Bank Digital Currencies (CBDCs)
CBDCs nau’ikan kuɗaɗen digital ne da a ke samar da su akan blockchain
kamar yadda a ke samar da kowanne cryptocurrency akan blockchain,
sai dai masana ba su cika sanya su a jerin nau’ikan cryptocurrency ba
sakamakon bambancin su da kuɗaɗen digital ɗinmu na gargajiya da
Gwamnati ke samarwa kaɗan ne. Bambancin su kawai su CBDCs ana
samar da su ne akan blockchain yayin da kuɗaɗen digital ɗinmu na
gargajiya ba sa aiki akan blockchain. Sai dai wasu daga cikin masana
suna kallon su a matsayin cryptocurrency kasancewar suna akan
blockchain kamar yadda cryptocurrencies su ke.
Gwamnatocin ƙasashe da yawa sun fahimci amfanin blockchain amma
suna faɗa da cryptocurrencies sakamakon cryptocurrency suna
wanzuwa ne a tsarin decentralization ta yadda Gwamnati ba za ta iya
sarrafa su, kula da su ko juya al’amuransu ba. Sakamakon haka sai
gwamnatocin ke ƙirƙirar nasu cryptocurrencies ɗin wanda su ke akan
tsarin centralization ta yadda zai kasance Manyan Bankunan ƙasashe ne
ke; samar da su, sarrafa su da kula da mu’amalolin da a ke yi da su. E-
Naira da Babban Bankin Nijeriya ya samar misali ne na nau’ikan CBDCs.


Leave a comment