TYPES OF CRYPTOCURRENCY
Duk da ya ke yanzu haka akwai fiye da nau’ikan cryptocurrencies 15,000 a kasuwa, sai dai masana na raba cryptocurrencies gida shida (6) bisa la’akari da manufar da aka samar da su da kuma wuraren da su
ke aiki. Ga su kamar haka:
1. Payment tokens
2. Privacy tokens
3. Utility tokens
4. Stablecoins
5. Central bank digital currencies (CBDCs)
6. Non-fungible tokens (NFTs)
Payment Tokens
Payment tokens nau’inkan cryptocurrencies ne da ke ɗaukar matsayin kuɗaɗe, ana samar da su ne musamman domin a ke amfani dasu wajen biyan kuɗi yayin cinikayya. Duk da ya ke, kowanne cryptocurrency za a iya amfani da shi a sayi wani abu da shi idan mai sayar da abin ya yarda a ke biyansa da irin coin ɗin, amma akwai nau’ikan cryptocurrencies ɗin da an ƙirƙire su ne musamman domin haka. Irin waɗannan nau’ikan cryptocurrencies suna ɗaukar matsayin kuɗaɗe ne irin waɗanda aka yi amfani da su a ƙarnin baya, ba irin kuɗaɗen takarda da ba a ajiyarsu a
matsayin kadara ba.
Mutanen ƙarnin baya sun yi amfani da; zinare, gishiri, tagulla, tasa a
matsayin kuɗi. Dukkanin abubuwan nan suna ɗaukar matsayin kuɗi
kuma suna ɗaukar matsayin kadara, kamar haka payment token su ke a
duniyar cryptocurrency. Suna ɗaukar matsayin kuɗi domin ana amfani
da su wajen saye da sayarwa, suna kuma ɗaukar matsayin kadara domin
ana iya sayen su da niyyar gaba a sayar aci riba, kamar yadda zinare ma
ana iya amfani da shi a sayi kaya kuma ana iya sayensa a ajiye a matsayin
kadara.
Privacy Tokens
Privacy tokens nau’ikan cryptocurrencies ne da a ke samar da su
musamman domin yin mu’amalolin kuɗaɗe cikin sirri ta yadda ba za a
ga mu’amalolin da aka yi da su ba. Privacy tokens sun bambanta da
sauran cryptocurrencies da a ke iya ganin bayanan mu’amalolin da a ke
yi da su a fayyace, domin idan na tura maka privacy token to ni da kai
ne ƙadai za mu san mu’amalar da muka yi amma wani ba zai iya dubawa
ya gani ba.
Galibin cryptocurrencies suna da tsarin fayyace mu’amala ta yadda
kowa zai iya duba adadin yawan coins ɗin da ya ke cikin wata wallet,
amma wanda ke da wallet ɗin ne kawai ba za a iya sani ba. Ta hanyar
amfani da privacy tokens kuwa, wani ba zai iya duba adadin coin ɗin da
aka tura ko aka ƙarba ba, sai waɗanda suka yi mu’amalar ne kaɗai za su
sani.
Yau munyi bayanin biyu daga cikin ire iren cryptocurrency token ko coins da muke da su, inshaAllahu gobe zamu kara bayanin guda biyu. An bani shawara akan takaita rubutun shine zai sanya a fahimta ni kuma so nake kowa ya fahimta.


Leave a comment