CRYPTO: DARASI NA 3

CHAPTER 02
INTRODUCTION TO CRYPTOCURRENCY
A yanzu muna zamani ne na fasahar kimiyya da ƙirƙira, ko da yaushe ƙara samar da sabbin dabarori da tsare-tsare a ke domin a kawo canji mai ma’ana a tsarukan mu’amalolin da mu ke yi yau da kullum. Kafin zuwan internet muna gudanar da rayuwa ne a gargajiyan ce, da zuwanta
sai ta canja fasalin yadda mu ke gudanar da kowanne fanni na rayuwarmu tun daga; fannin sufuri, ilimi, tsaro, cinikayya har ma da ɓangaren lafiya. Sauƙaƙe ayyuka da samar da mafita ga matsalolin da al’umma ke fuskanta a duniyarmu ta zahiri ya sa internet ta zama ɗaya daga cikin abubuwan da al’umma ke buƙata domin su yi rayuwa cikin sauƙi.
A ɓangaren kasuwanci da mu’amalolin da suka shafi kuɗaɗe, za mu iya ganin yadda internet ta kawo gagarumin canji da ci gaba wajen faɗaɗa kasuwancinmu da sauƙaƙe mana hanyoyin biyan kuɗaɗe. Domin internet ta zo ta iske muna amfani da nau’ikan kuɗaɗen zahiri wajen yin cinikayya (Fiat money), domin ƙara sauƙaƙe mu’amalolinmu na kuɗaɗe sai ta samar mana da digital money. A hankali ana ƙara samun ci gaba sai aka fahimci kuɗaɗen da mu ke amfani da su na digital, kuɗaɗe ne da ba su da bambanci da kuɗaɗen takarda ta fuska hawa kan tsarin ‘centralization’ wanda ya iyakance ikon gudanarwar kuɗaɗen a ƙarƙashin tsirarin mutane kaɗai. Hakan ya sa ba su gama cika sharuɗɗan zama ingantattun kuɗaɗe ba. Bugu da ƙari, kuɗaɗen digital suna da rauni ta fuskar tsaro da tauyewa al’umma ƴancin sarrafa dukiyoyinsu yadda su ke so ba tare da an gindaya masu dokokin da za su hana su walwala ba. To dama! idan ka ba wa wasu tsairarun al’umma cikakken ikon gudanar da kuɗi su kaɗai dole a samu matsaloli masu tarin yawa. Daga cikin matsalolin da al’ummah ke fuskanta a sanadiyyar
amfani da kuɗaɗen Gwamnati akwai:
● Rashin cikakken ƴancin da mutane ke da shi akan kuɗaɗensu ta yadda kai da kuɗinka amma ba ka da ikon amfani da su yadda ka ke so dole sai an gindaya maka sharaɗoɗi da dokokin da za ka kiyaye su a hukumance.
● Wahalhalun canjin kuɗaɗe musamman ga Ƴan kasuwar da ke zuwa saro kaya a wasu ƙasashen, ba su da damar amfani da
kuɗin ƙasarsu wajen sayo kaya a wata ƙasar.
● Tsadar kuɗin cajin da a ke yiwa mutane yayin gudanar da mu’amalolin kuɗi da suka haɗa da; adana kuɗaɗe a bankuna, tura kuɗaɗe ko karɓar su.
● Rashin sirrin mallakar kuɗaɗe ta yadda idan kana da kuɗi a banki, hukumomi da Gwamnati kan iya sanin nawa ka mallaka
har ma idan Gwamnati ta so tana iya hana ka yin amfani da kuɗaɗen naka.

Waɗannan matsalolin dama waɗanda ban lissafo ba suna daga cikin dalilin da masana suka ga cewar akwai buƙatar samar da samfurin kuɗin digital da za su taimaka a kawar da ƙalubalen da al’umma ke fuskanta a ɓangaren mu’amalolin da suka shafi kuɗaɗe. Domin kawar da ƙalubalen kuwa, dole sai an ɗauko tsohon tsarin samar da kuɗi na ‘decentralization’ sannan a samar da kuɗin da ke da halaye irin na zinare da za a iya amfani da su akan internet domin sauƙake wahalhalun zirga-zirga da su. Wannan ƙudiri shi ya haifar da samuwar
cryptocurrency.

What is Cryptocurrency?
Cryptocurrency nau’i kuɗaɗen digital ne masu zaman kansu, da su ke ɗaukar matsayin kuɗaɗen saye da sayarwa ko kuma kadarori da a ke kasuwancinsu akan internet. Bambancin cryptocurrency da kuɗaɗen digital da mu ke amfani da su shi ne: kuɗaɗen digital da mu ke amfani da su ikon samar da su da gudanar da su yana hannun Gwamnati da cibiyoyin kuɗaɗe, yayin da cryptocurrency kuma ikon samar da su da gudanar da su yana ƙarƙashin ilahirin al’ummar da suka yarda da su kuma suka amince su karɓe su a matsayin kuɗaɗe ko kadarorin da za a iya hada-hadarsu. Tsarin cryptocurrency da gudanarwar su yana kama da na zinare, kasancewar shi ma zinare yana ɗaukar matsayin kuɗi sannan yana ɗaukar matsayin kadara wanda a ke iya saye ko sayarwa.

Characteristics of Cryptocurrency
Cryptocurrencies a matsayin kuɗaɗe ko a matsayin kadarori suna da siffofi da tsarukan da su ke wanzuwa akan su. Ga su kamar haka:
● Digital
● Decentralised
● Pseudonymous
● Transparency
● Global
● Limited Supply
Digital
Cryptocurrency suna wanzuwa ne a siffar lambobi da za a iya turawa ko karɓar su ta hanyar amfani da internet, hakan na nufin babu su a zahiri, babu kuɗin takardarsu ko kuma tsabobinsu. Kasancewar su digital ya sa suna da sauƙin ɗauka a je duk inda a ke so ba tare da wani ma ya san akwai su ba. Ta wannan fannin za a iya cewa cryptocurrencies sun fi zinare sauƙin ɗauka da sauƙin ajiya domin shi zinare yana da gangar jiki kuma ana iya taɓa shi ko riƙe shi ba kamar cryptocurrency da ke a siffar
lambobi ba.
Decentralised
Cryptocurrencies suna wanzuwa ne akan tsari mai ƴanci wanda babu wata hukuma ko Gwamnatin da ke da ikon kula da mu’amalolin da a ke yi da su ita kaɗai. Kowa na iya samar da su matuƙar dai al’umma sun yarda da su to za a iya mu’amala da su a matsayin kuɗaɗe ko kadarori.
Ta fuskar adana bayanansu ma, babu wani rumbun ajiyar bayanai na wata Gwamnati ko wata hukuma da ke adana bayanan mu’amalolin da a ke yi da su.
Pseudonymous
Cryptocurrencies suna ɗauke da cikakken sirrin mallaka ta yadda za ka iya turawa ko a turo maka su ba tare da sunanka ko bayananka sun fito ba. Ba kamar kuɗaɗen gargajiya ba da kafin ka iya tura su ko ajiye su a cikin asusunka dole kana buƙatar buɗe account na banki, yayin buɗewar kuma sai an buƙaci; cikakken sunanka, adireshinka,
shekarunka, jinsinka har ma da katin shaidarka duk domin a iya gane ka
a kuma iya gane mu’amalolin da ka ke yi, sannan idan za a bincike ka a iya samun bayananka cikin sauƙi. Su kuwa cryptocurrencies wajen amfani da su ba ka buƙatar sanya bayananka sannan idan ka tura su ko kuma an turo maka ba za a taɓa iya gane cewa kai ne ka tura ko kuma
kai aka turowa ba. Duk mu’amalolin da ka yi da cryptocurrencies daga kai sai Allan da ya halicce ka ne kawai ku ka sani, bayan ku babu mai sani ko da ya bincika. Idan za ka saye su za ka saye su ne ba tare da sanin
wajen wanda ka saya ba, idan za ka sayar da su za ka sayar da su ne ba tare da ka san wanda ka sayarwa ba.
Transparency
Duk da an samar da cryptocurrency da cikakken tsarin ɓoye bayanan masu gudanar da mu’amaloli, amma kuma suna da sigar fayyace duk mu’amalolin da aka yi da su. Yayin gudanar da mu’amaloli da
kuɗaɗenmu na gargajiya bankuna ne ke ajiye bayanan tarihin mu’amalolin da aka yi, bankunan ne kaɗai ke damar kallon mu’amalolin da mutane su ke yi da kuɗaɗensu. Amma cryptocurrencies kuwa, babu wata cibiya da ke adana bayanan mu’amalolin da aka yi da su, maimakon hakan bayanan na warwatse ne a kowacce computer ko wayar da a ke amfani da ita wajen yin mu’amalolin da suka shafi
cryptocurrency ɗin. Saboda haka, kowa zai iya ganin cryptocurrency ɗin da aka tura daga wata wallet zuwa wata wallet, amma babu wanda zai iya gane wanda ya tura da wanda aka turawa. Hakan na nufin, cryptocurrency a bayyane su ke kuma a boye su ke. za a iya ganin adadin
cryptocurrency ɗin da ke cikin kowacce wallet ma, idan mai wallet ɗin ya tura cryptocurrency zuwa wata wallet, za a ga turawar da adadin yawan cryptocurrency din da aka tura, lokacin da aka tura har ma kuɗin cajis ɗin da aka caji wanda ya tura. Sai dai ba za a iya gane wanda ya tura da wanda aka turawa ba.
Global
Kamar yadda a lokacin da a ke amfani da zinare a matsayin kuɗi ko ina kika je a faɗin duniya za ki iya cinikayya da zinare ba tare da kin buƙaci yin canji ba, haka su ma cryptocurrencies a ko ina kike a faɗin duniya za ki iya mu’amala da su. Saboda cryptocurrency ba kuɗin wata ƙasa ba
ne ballantana ya zamanto a iya ƙasar kaɗai za ki iya kashe su, su kuɗin al’umma ne da za ki iya kashewa a duk inda al’umma su ke a faɗin duniya matuƙar dai al’ummar sun yarda da su. Ba sa kuma dogaro da tattalin arziƙin wata ƙasa ballantana idan tattalin arziƙin ƙasar ya karye hakan ya shafi ƙimarsu, su suna amfani ne da tattalin arziƙin kansu dakansu. Bugu da ƙari, kasuwancin su bai keɓanta da wata ƙasa ƙadai ba, idan kina da su za ki iya sayarwa mutumin da ke a wata ƙasar daban,
kuma ke ma za ka iya saye daga mutumin wata ƙasar.
Limited Supply
Ba kamar kuɗaɗenmu na gargajiya da Gwamnati kan iya buga duk adadin da ta ke so idan ta buƙaci hakan ba, kowanne cryptocurrency na zuwa ne da ƙayyadadden adadin (Total supply) da yawansa ba zai taɓa wuce wannan adadin ba. Misali: adadin yawan Bitcoins guda 21,000,000 ne, saboda haka har abada Bitcoin zai tabbata ne a guda 21,000,000, ba zai taɓa wuce haka ba, ba ma zai taɓa ƙaruwa ko da da guda ɗaya kacal ba. Ƙayyadadden adadi da cryptocurrencies ke zuwa da su, yana daga cikin abin da ke sanyawa su ƙara daraja da baiwa masu kasuwancinsu damar samun riba a ƙanƙanin lokaci. Rashin ƙayyade adadin kuɗaɗenmu na gargajiya na daga cikin dalilin da ke sanyawa darajarsu ke raguwa. Da yawan mutane suna da tunanin cewa, tunda Gwamnati ce ke buga kuɗi to mai zai sanya Gwamnati ba za ta dinga bugawa tana rarrabawa al’umma don kawar da talauci ba? Masu irin wannan tunanin ba su
fahimci cewa darajar kuɗi na ƙaruwa ne idan adadin kuɗin ya yi ƙaranci a hannun al’umma ba. Idan ya kasance kuɗaɗe suka yi yawa a hannun mutane, buƙatar kuɗin domin yin cinikayya ta ragu to darajar kuɗin ma za ta ragu. Ya ki ke kallo idan ya kasance kowa ya noma masara a Nijeriya? Idan kowa ya noma masara to tabbas buƙatar sayen masara dole za ta ragu, don haka farashin masarar ma dole ya ragu. Saboda me? Saboda wa zai sayi abin da yana da wadatar sa? To kamar haka ne idan kuɗaɗe suka yi yawa a hannun al’umma, darajarsu za ta ragu gwargwado yawan da suka yi a hannun al’ummar. Yadda ƙayyadadden adadin cryptocurrencies ke taimaka masu wajen ɗaga darajarsu shi ne, a lokacin da cryptocurrency ya ke sabo, mutanen da suka mallake shi za ka ga ba su da yawa sosai, saboda haka ba zai yi daraja sosai ba. Amma daga baya cryptocurrency ɗin na samun ƙarɓuwa adadin masu buƙatarsa na ƙaruwa, darajarsa da farashinsa ma za su
dinga ƙaruwa.

Pros and Cons of Cryptocurrency
Cryptocurrency na ɗauke tarin fa’idodi da waraka akan matsalolin da suka shafi Kasuwanci da mu’amalolin kuɗaɗe, a wani ɓangaren kuma suna ɗauke da irin nasu matsalolin da amfani da su zai iya haifarwa.

Pros
✓ Reducing corruption
✓ Eliminating extreme money printing
✓ Giving people charge of their own money
✓ Cutting out the middleman
✓ Serving the unbanked
✓ Borderless Transactions
✓ Liquidity

Reducing Corruption
Yayin da ka ba wa wani mutum ko wasu mutane cikakken iko akan wani abu fiye da sauran mutane to ka buɗe ƙofar cin hanci da rashawa kenan. Kasancewar kuɗaɗenmu na gargajiya da mu ke amfani da su ikon samar da su, sarrafa su da kula da su yana hannun tsirarrun mutane, hakan babbar barazana ce da za ta iya haifar da cin hanci da rashawa, domin tsirarun mutanen za su iya cin karansu babu babbaka saboda fura da ludayi na hannunsu, yadda suka dama haka kowa zai sha. Amma cryptocurrencies sarrafa su, samar da su da kula da bayanan mu’amalolin da a ke yi da su duk yana hannun al’umma ne, babu wata cibiya ko wani mutum da ke da iko fiye da na sauran al’umma ballantana ya yi amfani da wannan damar wajen yin almundahana, alfarma ko
karkatar da kuɗaɗen al’umma.
Amfani da cryptocurrency zai taimaka sosai wajen kawar da cin hanci da rashawa. Misali, idan Gwamnati ta ware kuɗi domin yin wani aiki, matuƙar kuɗaɗen cryptocurrency ne kuma aka faɗi wallet address ɗin da aka sanya su, hakan zai ba wa al’umma damar bibiyar duk abin da a
ke yi da su . Da zarar an ciri kuɗi daga wallet ɗin jama’a za su gani an cira, za su ga lokacin da aka cira, za su ga wallet ɗin da aka turawa sannan za su iya ganin nawa ne ya rage a cikin wallet ɗin. Ba kamar yadda ya ke idan an ware kuɗaɗen gargajiya domin gudanar da wani aiki ba, wani lokacin ma Gwamnati na rasa wa ya cire kuɗin kuma ko da an bi diddigi to yana ɗaukar lokaci mai tsayi kafin a gane. Ta hanyar amfani da cryptocurrency, idan Gwamnati ta so bincikar yadda aka kashe wasu kuɗaɗe da aka ware domin yin wani muhimmin aiki, a cikin minti biyu za a iya tattara bayanan yadda aka kashe kuɗin ba tare da ɓata lokaci ba.

Eliminating Extreme Money Printing
Amfani da cryptocurrency zai taimaka wajen rage buga kuɗi ba bisa ƙa’ida ba da Gwamnati ke yi wanda hakan ke haifar da karyewar darajar kuɗaɗen. Galibi, idan ƙasa na fuskantar matsin tattalin arziƙi sai Gwamnati ta umurci Central Bank da ya buga takardun kuɗaɗe da yawa da niyyar a rarrabawa ƴan ƙasa bashin kuɗaɗen domin farfaɗo da tattalin arziki a cikin kasar. Sai dai wannan tsarin bai cika haifar ɗa mai
ido ba, domin kamar ɗaure rauni ne da tsumma wanda ba ya hana a ji zafin raunin. Misali, idan Gwamnatin Nijeriya ta buga takardun kuɗaɗe da yawa adadin kuɗaɗen za su yawaita a hannun mutane sai darajar
Naira ta karye, idan darajar Naira ta karye kuwa hakan zai haifar dahauhawar farashin kayayyaki wanda zai jefa ƴan Nijeriya cikin ƙuncin rayuwa sannan ya ƙara jefa ƙasar cikin matsanancin karayar tattalin arziki.
Bisa al’ada, kowanne cryptocurrency yana da ƙayyadadden adadi, ta hanyar amfani da cryptocurrency Gwamnati ba za ta dinga buga kuɗaɗe duk shekara ba, hakan zai taimaka wajen ɗaga darajar kuɗin ƙasar
sannan Gwamnati za ta daina kashe maƙudan kuɗaɗe a ƙoƙarin buga sabbin kuɗaɗe kamar yadda ta ke yi kusan kowacce shekara. Misali: a shekara 2020 kaɗai, Babban Bankin Najeriya ya kashe Naira biliyan 58.618 wajen bugo takardun kuɗaɗe guda biliyan 2.518 wanda darajarsu ta kai tiriliyan 1. A shekarar 2019 ma Babban Bankin ya kashe Naira biliyan N58.618, yayin da a shekarar 2018 kuma ya kashe kimanin
Naira biliyan N75.523 duk a ƙoƙarin bugo sabbin takardun kuɗaɗe. Irin wannan maƙudan kuɗaɗe da a ke kashewa ta hanyar amfani da cryptocurrency ba za a kashe su ba, maimakon haka sai dai a yi amfani da su wajen ayyukan raya ƙasa.

Giving People Charge of Their Own Money
Amfani da cryptocurrency zai taimakawa al’umma su sami cikakken ƴancin sarrafa kuɗaɗensu yadda su ke so ba tare da an gindaya masu dokoki ba; za su iya tura duk adadin da su ke so ba tare da an ƙayyade
masu adadin da za su iya turawa ko wacce rana ba, za su iya ajiye duk adadin kuɗaɗen da su ke so ba tare da ƙayyade masu adadin da za su iya ajiyewa ba, kamar dai yadda ya ke faruwa a bankunanmu na gargajiya.
Ta hanyar amfani da kuɗaɗen gargajiya kuwa, al’umma ba su da ikon sarrafa kuɗaɗensu yadda su ke so sai yadda Gwamnati ta ke so. Kai da kuɗinka ba ka da ƴancin cirewa a duk lokacin da ka ke so, ba ka da ƴancin tura adadin yawan kuɗin da ka ke so, sannan ba ka da ikon ajiye duk yawan adadin kuɗin da ka ke so, sai abin da Gwamnati ta ƙayyademaka za ka iya: ajiyewa, cirewa ko turawa a kowacce rana, idan Gwamnati ta ga dama ma kai da kuɗinka sai ta hana ka amfani da su.

Cutting Out the Middleman
Idan kana son tura wa wani kuɗi, dole kana buƙatar banki a matsayin wanda zai tura maka kuɗin zuwa asusun wanda ka ke son tura wa. Shigowar banki a tsakanin mai turawa da mai karɓa shi ke haifar da
jinkiri domin kafin bankin ya gama bincikawa tare da tantance ingancin mu’amalar sai ya ɗauki ɗan lokaci, ba kamar tura cryptocurrency da ke faruwa tsakanin mai turawa da mai karɓa ba tare da wani a tsakiyar su ba. Bugu da ƙari, yayin saye ko sayar da kadara ta zahiri, kamar gida,
filaye da dai sauransu, mai saye da mai sayarwa suna buƙatar Dillali ko Lauya ko kuma duka biyun a tsakaninsu. Shigowar Dillali ko Lauya a tsakanin mai saye da mai sayarwa na haifar da jinkiri. Bayan jinkiri ma,
dole mai saye da mai sayarwar sai ko wanensu ya biya Dillali ko Lauya da suka taimaka wajen sasanta cinikayyar da tabbatar da doka a tsakani. Ta hanyar amfani da cryptocurrency kuwa; za ka iya sayen cryptocurrency na biliyoyin kuɗaɗe ba tare da wani ma ya sani ba ballantana buƙatar lauya ko dillali ta shigo ciki. Za ku gudanar da cinikayyar ne tsakanin ka da mai sayarwar ba tare da wani ya shigo ciki ba, abin burgewar ma har ka saya ka biya kuɗin ba za ka san wajen wanda ka saya ba shi ma kuma ba zai san wanda ya sayar wa ba.

Serving The Unbanked
Sakamakon binciken Global Finance and Merchant Machine na 2021 ya nuna, a halin yanzu akwai kimanin mutane biliyan 2 da ba su da asusun banki a faɗin duniya. A Nijeriya kuma waɗanda da ba su da asusun ajiyar
kuɗi a banki sun kai mutum miliyan 123.6 watau kimanin 60% kenan na yawan mutanen Nijeriya. Galibin mutane ba sa samun damar mallakar asusun ajiya a bankuna ne sakamakon rashin cika ƙa’idodin buɗe asusun banki, wasu kuma saboda rashin kuɗi sakamakon buɗe asusun na buƙatar kuɗin da ba za su iya biya ba. Misali: kafin buɗe asusun banki ana bukatar hotunan passport guda biyu, domin yin hotunan nan kuwa sai ka kashe a ƙalla N500, sannan ana buƙatar a ƙalla N2,000 da za ka sanya a asusun wanda galibin mutane suna fama da abin da za su ci ma ballantana su iya biyan wannan kuɗaɗe.
Amfani da cryptocurrency ba ya buƙatar buɗe asusun banki, abin da ya ke buƙata kawai shi ne: mallakar waya ko computer. Yayin buɗe wallet kuma ba a buƙatar ka sanya ko da sunanka ko katin shaidar ka
ballantana rashin katin sheda ya hana ka buɗewa. Ashe kuwa, cryptocurrency zai taimakawa waɗanda ba su da damar buɗe asusun banki, ta hanyar amfani da cryptocurrency kowa ma zai iya turawa ko a turo masa matuƙar dai ya san yadda a ke yi.

Borderless Payment
Amfani da cryptocurrency zai taimaka wajen cire wahalar yin mu’amalar kuɗaɗe tsakanin ƙasashen waje. Misali: idan kana da cryptocurrency a Nijeriya za ka iya zuwa Saudia ka sayar da shi ba tare da ka yi canjin kuɗi ba. Da yawan mutane ma suna amfani da cryptocurrency ne domin kawar da matsalar yin canji da wahalar tura kuɗi zuwa wata ƙasar. Maimakon da za ka tafi Saudia ka yi canji, sai kawai ka bari idan ka isa sai ka sayar da cryptocurrency ɗinka a biya ka da kuɗin Saudia ɗin. Sannan za ka iya mallakar katin cire kuɗin cryptocurrency da zai ba ka damar cire kuɗi a duk ƙasar da ka je.Idan ya kasance kuma Ƴan kasuwa ba sa buƙatar yin canjin kuɗaɗe idan za su sayo kaya daga ƙasashen ƙetare, hakan zai taimaka wajen rage tashin kayan masarufi wanda ƙarancin Dollar ke haifarwa. A nan Nijeriya amfani da cryptocurrency zai iya taimaka wa wajen haɓɓaka darajar Naira, idan Ƴan kasuwarmu suka gane yin mu’amalar kuɗi da cryptocurrency hakan zai rage yawan buƙatar dollar domin zuwa yin sayayya a ƙasashen waje, rage buƙatar Dollar kuwa zai sa darajarta ta karye idan za a canja ta da Naira.

Liquidity
Ba kamar kadarorin zahiri da idan kana buƙatar sayar da su sai ka jira mai saye ba, ko idan kana buƙatar saye sai ka jira mai sayarwa ba. Idan kana da cryptocurrency kuma kana buƙatar saye ko sayarwa za ka iya saye ko ka sayar nan take.
Liquidity kuɗi ne da a ke sanyawa a kasuwar cryptocurrency ta yadda mai sayarwa zai iya sayar da cryptocurrency ɗinsa akan farashin da ya ke ba tare da ya jira mai saye ya buƙaci saya ba, idan kuma kana ɓukatar
saye ne to za ka iya saye ba tare da jiran mai sayarwa ba. Bugu da ƙari, kasuwar cryptocurrency tana ci 24/7, babu lokacin da a ke rufewa ko buɗe kasuwar saboda ita ko da yaushe a buɗe ta ke. Idan kana son sayen cryptocurrency to za ka iya saya a kowanne lokaci kuma a duk inda ka
ke a faɗin duniya, idan kana son sayarwa ma za ka iya sayarwa a kowanne lokaci kuma nan take.
Liquidity da cryptocurrencies su ke da shi yana daga cikin abin da ya sa suka zama kadara mafi daɗin sha’ani domin da zarar ka matsu to za ka iya matsar kayanka a kowanne lokaci. Amma kadarorin zahiri kamar gida ko fili a wani gurin sai a fi shekara ba a samu mai saye ba, idan ka
matsu kuma sai dai ka sayar asara. Misali: wani lokacin za ka ga iyaye suna son aurar da ƴarsu saboda haka sai su ɗaga fili da niyyar sayarwa,amma a ƙarshe sai dai a dinga ɗaga ranar auren saboda rashin mai sayen filin. Ko kuma wani ya buƙaci sayar da wata kadararsa domin biyan kuɗin jinyar da ta ke buƙatar kulawar gaggawa, a ƙarshe har mara lafiyar ma zai mutu ba tare da a samu mai saye ba.

Cons
● No reverse of payment or recovery
● Volatile in nature
● Black market

No Reverse of Payment or Recovery
Ba kamar kuɗaɗen gargajiya da idan ka tura kuɗi suna iya dawowa ba, sannan idan ka yi kuskure wajen turawar kana iya zuwa banki ka yi ƙorafi a nemi wanda ka turawa har dai a ƙarshe a dawo maka da kuɗaɗenka. Su cryptocurrencies idan an tura su ba sa taɓa dawowa kuma ba a taɓa dawo da su. Ɗabi’arsu ta ɓoye bayanan masu mu’amala
da su ya sa ba za a iya gane wanda ka turawa ba ballantana a sanya ya dawo da su. Hakan na nufin idan ka yi kuskure wajen turawa to ka yi asararsu kenan domin ba za ka iya dawo da su ba sannan su ma ba za su dawo ba. Bugu da ƙari, a wajen buɗe wallet ba a amfani da bayanan mutum, saboda haka idan wayarka ko computer naka ta faɗi ko ta lalace kuma ya kasance ba ka ajiye private keys naka ba to ka yi asararsu kenan. Sannan ko da biliyan nawa ka ke da su na cryptocurrency matuƙar babu wanda ka faɗawa private keys naka idan ka mutu magada ba za su iya amfani da su ba. Amma ta hanyar amfani da bankuna idan ka mutu ‘Next of kin, naka zai iya zuwa ya buƙaci kuɗin kuma a ba shi.

Volatile In Nature
Hawa da saukar farashin cryptocurrency da ke aukuwa lokaci bayan lokaci yana iya zama alheri sannan yana iya zama sharri. Darajar cryptocurrency a kasuwa ba ta da tabbas, za ka iya ajiye cryptocurrency na milliyan ɗaya ka ga ya koma na ƙasa da dubu ɗari, duk da ya ke ya danganta da irin cryptocurrency ɗin da ka ajiye. Sannan za ka iya ajiye coin na dubu ɗari ka zo ka iske ya koma na million ɗaya. Ba kamar kuɗaɗenmu na gargajiya ba, idan ka ajiye kuɗinka a banki darajar su ba za su ragu ba sai idan bankin ne ya cira.

Black Market
Ɗabi’a cryptocurrency na ɓoye bayan masu mu’amala zai iya taimakawa masu aikata miyagun laifi kamar; ƴan ta’adda, masu fataucin miyagun kwayoyi da sauransu. Ta hanyar amfani da kuɗaɗen gargajiya, ƴan
ta’adda na shan wahalar gudanar da mu’amalolin kuɗi domin ana iya bin diddiginsu a gano su cikin sauƙi. Amma ta hanyar amfani da cryptocurrency, ƴan ta’adda na iya sayen makamai su biya ba tare da an iya gano su ba. Bugu da ƙari, ta wani ɓangaren cryptocurrency zai iya taimakawa ɓarayin Gwamnati musamman idan ya kasance Gwamnatin ba ta karɓi tsarin amfani da cryptocurrency ba. Misali: anan Nijeriya ƴan siyasa na iya satar kuɗi su sayi cryptocurrency su ajiye ba tare da EFCC ta iya ganowa ba, ba kamar yadda idan sun ajiye kuɗaɗe a banki ko kuma sun sayi kadarori EFCC ke iya bin diddiginta ta gano ba. Amma idan ya kasance Gwamnati na amfani da cryptocurrency ne kuma aka
ware cryptocurrency aka ba wa wani ɗan siyasa domin ya yi aiki, to ana iya ganin yadda ya ke kashe kuɗin ta yadda ba zai iya sata ba don ko da ma ya sata za a gane.

InshaAllahu darasinmu na gaba zai fara ne daga ‘Types Of Cryptocurrencies’ sannan kuma ina sanar daku cewa inshaAllahu dagawannan satin zamu fara gabatar da darasi sau biyu a sati (Ranar laraba da

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started