PART ONE
THE ART OF HODLING
Takaitaccen tarihin crypto currency
An fara yunƙurin samar da kuɗaɗen internet ne tun a 1990s, lokacin da ƙwararren masanin ilimin cryptography nan ɗan asalin kasar America watau David Chaum ya ƙirƙiri kuɗin internet na farko a ƙasar Netherlands. David ya samu nasarar ƙirƙirar DigiCash ne ta hanyar amfani da fasahar Encryption algorithm na RSA domin ba shi cikakken
tsaron adana bayanai da kuma tantance mu’amalolin da a ke yi da shi.
DigiCash ya ɗauki hankullan kafofin yaɗa labarai musamman saboda kasancewar shi kuɗin internet na farko da aka fara samarwa. Ba a jima ba ya samu ƙarɓuwa da hasken goshi wajen al’umma har ta kai
kamfanin Microsoft Corporation ya taya shi akan zunzurutun kuɗi har $180,000,000 da niyyar ɗora shi akan kowacce computer da ke aiki da windows operating system. Sai dai David Chaum da kamfaninsa ba su
amince da tayin ba, wanda rashin amincewa da tayin kuwa na daga cikin manyan kurakuren da David Chaum da kamfaninsa suka aikata da yai sanadiyyar rushewar DigiCash.
Yunƙuri na biyu na samuwar kuɗin internet an ƙirƙiro shi ne daga faɗaɗa bincike da nazari akan tsarukan DigiCash. Kamfanoni daban- daban daga baya sun duƙufa wajen ƙoƙarin ganin sun samar da kuɗaɗen
internet tare da kawo canje-canje masu ma’ana na zamani wanda DigiCash bai zo da su ba. Daga cikin kamfanonin akwai: PayPal, wandashi ne ya fi shahara da samun ƙarɓuwa a wajen al’umma. Dalilin da ya
sa ya ciri tuta a tsakanin sauran kamfanonin shi ne: saboda ya ba da damar a yi amfani da shi a dandamalin yanar gizo (Web browser) wanda hanya ce da mutane suka fi sabawa da ita. PayPal na da bambanci da
sauran kamfanonin masu gasa da shi, masu amfani da PayPal kan iya tura kuɗi ko karɓar ta amfani da tsarin sadarwa na peer-to-peer. Ya kuma taka muhimmiyar rawa wajen zamantar da harkokin biyan kuɗi na internet musamman tsarin amfani da katin cire kuɗi (Credit card) wanda masu amfani da PayPal kan iya mallaka kuma su cire kuɗi a duk inda su ke a faɗin duniya ba tare da la’akari da bambanci ƙudaɗe ba.
Nasarar da PayPal ya samu ce ta ƙara zaburar da wasu kamfonin wajen ƙoƙarin ganin sun samar da irin nasu tsarin biyan kuɗi na internet domin su yi goyayya da shi, daga cikin kamfanonin akwai; E-gold, B-Money, Bit Gold da dai sauransu.
Babban muhimmin abu na gaba a cikin tarihin cryptocurrency shi ne a October 31, 2008 wani mutum da har yanzu ba a san takamaiman waye shi ba mai suna ‘Satoshi Nakamoto’ ya fitar da wata takarda (White
paper) da ke ɗauke da bayani daki-daki na fasahar da a yanzu mu ke kira da “Blockchain” Samuwar fasahar blockchain ne ya haifar da samuwar dukkanin
nau’ikan kuɗaɗen da mu ke kira “Cryptocurrency” Ta hanyar amfani da
blockchain ne aka samar da kuɗin Bitcoin.
Wanda yanzu haka akwai fiye da adadin Bitcoin 18,000,000 da ke zagayawa a hannun mutane wanda ƙimar kuɗinsu ya kai kimanin $1,000,000,000,000,000.
An fara kasuwancin Bitcoin ne a July, 2010, kowanne Bitcoin ɗaya bai wuce N5 ba a lokacin. Amma a yanzu da na ke maganar nan shekara 13 ke nan da samuwar Bitcoin, farashin kowanne Bitcoin ɗaya ya haura
N14,500,000. Wanda ya sayi Bitcoin na kimanin N100 kacal a July, 2010 zuwa yanzu yana da ribar fiye da N610,000,000.

CHAPTER 01
MONEY
Abu ne mai wuya ku fahimci yadda cryptocurrencies su ke, yadda su ke
aiki da yadda a ke kasuwancinsu idan ba ku san yadda kuɗaɗe su ke a ilimance ba. Saboda haka ne ma, za mu waiwayi tarihin samuwar kuɗaɗe da yadda suka dinga chanjawa a lokutta daban-daban, tare da
yin bayani game da siffofin da ya kamata a ce kuɗaɗe su na da su kafin a kira su da kuɗaɗe masu inganci.
What Is Money?
Kuɗi na nufin duk wani abu da al’umma suka yarda su yi amfani da shi a matsayin abin da zai wakilci ƙimar kayayyakinsu da ayyukansu a mu’amalolinsu na saye da sayarwa. Kuɗi na ba wa mutane damar kwatanta ƙimar kayayyaki don sauƙaƙe cinikayya da adana dukiya yadda ya dace. Misali: kin ba ni kuɗi ni kuma na ba ki waya, abinci, sutura da dai sauran abubuwan bukata, kuɗin da kika ba ni shi ya wakilci darajar abinda na ba ki, ni ma zan iya amfani da kuɗin wajen sayen wani abin daban. A garuruwan da mu ke rayuwa, akwai mutane daban-daban da ke
ayyuka da sana’o’i daban-daban. Misali, idan ni marubucin littafin fi ne ke kuma ƙila noma kike yi, wata kuma malama ce, wata tela yayin da wata kuma kasuwanci take yi. A matsayina na marubuciyar littafi inabuƙatar cin abinci domin na rayu, sai dai ni bana noma ballantana na ke noma abin da zan ci. A matsayinki na mai yin noma ke ma kina buƙatar karanta litattafai domin ki samu ilimi. A wannan yanayi, ni da ke duka
muna buƙatar abubuwan da ba ma iya samarwa da kanmu dole sai mun naima a hannun junanmu. Tunda ina buƙatar abincin ci ke kuma kina buƙatar littafin karantawa ki samu ilimi, zan iya ba ki littafin ke kuma ki ba ni abincin da ya kai darajar littafina. To amma idan ya kasance ni ina buƙatar abinci ke kuma ba ka buƙatar littafina kuma fa? Kenan sai dai na daina rubuta littafi na koma yin noma idan ina son na rayu? Idan kowa ya koma noma ta ya za a samu; malamai, likitoci da masu ɗinkin kaya? Domin kawar da wannan matsalar sai mu samu wani abu daban wanda da ni da ke muka amince ya wakilci darajar kayayyakinmu, na ba ki abin ke kuma ki ba ni abinci. Idan kina buƙatar sayen takin zamani sai ke ma ki ba da abin a ba ka takin zamanin da ki ke buƙata. Wannan abin da muka amince da shi ya wakilci daraja da ƙimar kayayyakinmu ko da ganye ne to shi a ke kira da “Kuɗi”.
How People’s Trust In Money Has Evolved
A ƙarnukan da suka shuɗe, mutane sun yi amfani da abubuwan daban- daban a matsayin kuɗin cinikayya kamar; fata,gishiri, makamai, ƙarafuna, tasa, azurfa, tagulla, zinare da dai sauransu. Kafin wannan
lokacin mutane suna amfani da tsarin ban gishiri na ba ka manda
(Bartering system) wajen cinikayya: idan manomi na buƙatar fatanya sai ya ba da kayan da ya noma a ba shi fatanyar. Sai dai wannan tsari na yin musayar kayayyaki yana da wahalarwa sosai domin kafin manomin
ya samu wanda zai amince ya ƙarbi kayan gona ya ba shi fatanya sai ya wahala, ƙila ma sai ya ɗauki kayan gonar ya tafi kasuwa ya dinga cigiya, idan ma ya samu wanda zai karɓa ya ba shi fatanyar, to sasanta yawan
kayan gonar da zai ba shi ma wani jan aiki ne.A hankali sai mutane suka fara amfani da abubuwa masu darajar kamar gishiri, fata, makamai da dai sauransu a matsayin abubuwan da za su wakilci ƙimar kayayyakinsu. Idan manomi yana buƙatar fatanya sai ya
ba da gishiri a ba shi fatanya gwargwadon adadin da suka sasanta. Haka idan yana buƙatar sayar da kayan gonarsa sai ya bayar a ba shi gishiri ko dai duk wani nau’in abu da su ke amfani da shi a lokacin. Daga baya mutane suka fahimci amfani da wannan abubuwan ma akwai wahalarwa, sakamakon akwai abin da ba ya rabuwa ballantana ka raba ka sayi abin da bai kai darajar guda ɗaya ba, akwai kuma abubuwan da adana su da yawo da su babban jidali ne. A haka dai har aka zo zamanin amfani da zinare a matsayin kuɗin cinikayya. Amfani da zinare ya taiƙaita yawan wahalhalun da mutane ke fuskanta, kasancewar shi ba ya lalacewa kuma yana da sauƙin adanawa. Zamani na tafiya mutane na ƙara samun fasahohi tare da kawo abubuwan da za su sauƙaƙe wahalhalun da su ke yi, anan ne suka
fahimci shi kansa zinaren yana da wahalar cinikayya musamman idan kana son sayen abin da bai kai darajar sinƙin zinare ba. Hakan ne ya janyo samuwar tsabobin kuɗaɗen zinare ta hanyar sarrafa shi tare da samar da sulalansa domin sauƙaƙe wa mutane biyan ƙananun abubuwa ba tare da shan wahala ba. Ai kuwa kwalliya ta biya kuɗin sabulu domin mutane sun ɗauki tsawon shekaru suna amfani da sulallan zinare a matsayin kuɗaɗen cinikayya.
Ilimi na ƙara samuwa, hikimomin ƙirƙira na ƙara samuwa cikin al’umma, har aka zo zamanin da mutane suka sake fahimtar su ma tsabobin kuɗaɗen zinaren nan suna da nasu kalar wahalarwar: Idan kana son zuwa kasuwa sayen kaya masu yawa sai dai ka tafi da tarin sulala wanda ɗaukarsu kaɗai ma babban jidali ne, ga kuma ɓarayi akan
hanya idan sun tare ka ba za ka iya ɗaukar sulalan ka gudu ba sai dai kabar su a nan kai kuma ka tsira da rayuwarka. Sakamakon haka aka fara samar da bankunan ajiyar sulala, idan ka kai sulallanka sai a lissafa a ba ka takardar shaidar ajiya ka tafi da ita, idan kana son sayen abu maimakon bayar da zinare kana iya bayar da takardar shaidar ajiyar zinarenka a ba ka abin. A hankali a hankali amfani da takardar shaidar ajiyar banki ya mamaye ƙasashen duniya, duk da haka dai kana iya ba da tsabar kuɗi a karɓa. Haka mutane suka dinga amfani da takardar shaidar ajiya da kuma sulallan kuɗi wajen cinikayya, har zuwa zamani mulki mallaka da yaƙoƙin duniya wanda ya haifar da samuwar kasashe daban-daban. Kafin samuwar ƙasashen, ba gwamnatoci ne su ke bayar da takardar shaidar ajiya ba, bankuna ne ke bayarwa. Da ƙasashe suka samu ya kasance kowacce ƙasa tana da Gwamnatinta daban, sai aka samar da
kuɗin takardu wanda a ke kira da “Fiat money” Idan kuna fahimta zaku ga yadda kuɗaɗe suka dinga canjawa daga wani abu zuwa wani abu a ƙarnuka daban-daban. Abu ɗaya ne bai taɓa chanjawa ba: yarda. Dukkanin canje-canjen da aka dinga samu na abubuwan da a ke amfani da su a matsayin kuɗi ya faru ne saboda mutanen sun yarda su daina amfani da abu kaza su koma suna amfani da abu kaza, ashe dai kuɗi na nufin duk abin da al’umma suka yarda da shi.
Fiat Money
Kalmar “Fiat” ta samo asali ne daga yaren Latin wanda ke nufin “Abin da aka zartar” Ma’ana abin da Gwamnati ta sanya shi ya zama doka. Kuɗaɗen fiat, watau kuɗaɗen da mu ke amfani da su a yanzu, darajarsu
da ƙimarsu ta ta’allaƙa ne da zartarwar Gwamnati: ita ke da alhakin samar da su sannan ta zartar cewa kowanne ɗan kasa ya yarda da su a matsayin kuɗaɗen saye da siyarwa. Yardar mutane akan amfani da wani abu a matsayin kuɗi yanzun yardar
ta koma akan Gwamnati. Mutane sun yarda Gwamnatin ƙasarsu ta samar masu da abin da zai wakilci daraja da ƙimar kayayyakinsu da ayyukansu. Saboda haka Gwamnati ke buga kuɗaɗen takarda ta kuma ba su darajar da ta ga dama. Ita ke da alhakin cewa “Wannan takardar N1000 ce wannan kuma N100 ce” sai mutane su ke amfani da su a matsayin kuɗaɗen cinikayya. Kuma ita kaɗai ce ke da ikon buga kuɗaɗen da ƙayyade su izuwa duk adadin da ta ke so, yayin da ragowar mutane kuma ba su da ikon bugawa ko sarrafawa. Saɓanin ada kuma mutane na da ikon zaɓar abin da su ke so ya wakilci ƙimar kayayyakinsu sannan kowa na da ikon samar da wannan abin. Tsarin bai wa Gwamnati ikon kula da al’amuran kuɗi; samar da su, sarrafa su da ƙayyade adadinsu ita kaɗai shi a ke kira da da “Centralization” yayin da tsarin da
al’umma ke amfani da shi a baya da ya ba su ikon samar da abin da suka yarda da shi a matsayin kuɗi shi a ke kira da “Decentralization”.
Digital Money
Digital money ko digital currency na nufin duk wani nau’in kuɗi da a ke cinikayya da shi ta hanyar tura lambobin kuɗi maimakon takardarsu ko sulallansu, kamar dai kuɗin da mu ke turawa ko karɓa ta hanyar amfani
da banki. Samuwar internet ne ya wajabta samar da kuɗaɗen lambobi domin al’umma su ke amfani da su wajen cinikayya a internet ɗin. Guguwar sauyi da juyin juya hali da internet ta zo da shi wanda tai sanadiyyar sauya fasalin yadda mu ke gudanar da al’amuranmu na yau da kullum,
ya kasance duk wani abu da mu ke amfani da shi a zahiri ana ƙoƙarinsamar da irinsa a internet. Internet ta zama tamkar duniya ta biyu wadda mu ke rayuwa a cikinsu, muna zama a duniyarmu ta zahiri yayin da wasu al’amuran kuma muna gudanar da su ne a internet kamar; kafofin sadarwar zamani, kasuwanni da makarantun internet. Ashe
kuwa, matuƙar za mu iya ganin kaya mu saya a internet to akwai buƙatar ma a ce mu ke iya biyan kuɗin kayan a internet ɗin, wannan dalilin da makamancinsa ya sa aka samar da kuɗaɗen digital.
Duk da ya ke, galibin nau’in kuɗaɗen digital da mu ke amfani da su wajen saye da sayarwa su ma fiat money ne, bambancinsu kawai su lambobi ne ba takardu ko sulallai ba. Ta fuskar sauƙin mu’amala, tsaro
da sauƙin samarwa, kuɗaɗen digital sun fi kuɗaɗen takardu da sulallai da mu ke amfani da su sauƙi sha’ani. Saboda su lambobi ne, Gwamnati ba ta buƙatar kashe maƙudan kuɗaɗen buga su, sannan ba za su koɗe a sake bugo su ba. A yau 92% na kuɗaɗen da mu ke amfani da su wajen
cinikayya a faɗin duniyar nan duka nau’in digital money ne.
A hankali kuɗi na neman canja siffa daga takarda zuwa lambobi kamar
yadda ya canja siffa daga sulallai zuwa takardu. Ilimin da fasahar zamani ke sanyawa kudade ke canjawa, al’ummar kowanne ƙarni suna ƙoƙarin ganin sun samar da nau’in kuɗin da ya fi masu sauƙin sha’ani fiye da wanda suka saba amfani da shi. Idan kuna fahimta zaku ga
amfani da zinare a matsayin kuɗi ya fi amfani da gishiri sauƙin sha’ani,
amfani da sulallan zinare ya fi amfani da sinƙin zinari sauƙin sha’ani, amfani da kuɗaɗen takardu ya fi amfani da sulallai sauƙin sha’ani, yayin da amfani da kuɗaɗen digital kuma ya fi amfani da kuɗaɗen takarda sauƙin sha’ani.
Duk da ya ke masana ma suna ganin dama su kansu kuɗaɗen takardar ba takardun ba ne masu daraja, darajar kowanne kuɗin takarda yana a lambobin da su ke ɗauke da su ne. Misali, takardar N1000 ba ta fitakardar N100 daraja ba, illa lambar 1000 da ke cikin N1000 ne ya fi lambar 100 da ke jikin N100. Kasancewar su nau’in kuɗaɗen fiat watau kuɗaɗen doka wanda Gwamnati ta ke da ikon ba su duk darajar da ta ga
dama ta hanyar rubuta girman darajar a jikin lambobin da ke takardun. Takardun kuɗi suna a matsayin abin da mutane za su karanta su ga wacce daraja Gwamnati ta ba su ne. Da aka samar da computers da
wayoyin hannu ya kasance mutane suna iya karanta saƙonni da turawa ta cikin su sai aka ɗora lambobin kuɗi a cikinsu tunda dama amfanin takardun bai wuce don a karanta saƙon Gwamnati da su ke ɗauke da shi ba, kuma al’umma suna iya karantawa a computers ko wayoyin hannu. Idan kin nazarci wannan zaki ga ashe kuɗaɗen da mu ke amfani da su ba wasu abubuwa ne masu daraja ba illa zartarwar Gwamnati, sannan ba kuɗaɗen mu ke kashewa ba wannan dokar mu kewa biyayya. Misali, idan na sayi kaya a gurinki na ba ki kuɗin kayan
ko na tura miki, a zahiri kuɗaɗen nan babu abin da za ki iya sarrafawa da su, kawai kin amince ki karɓa ne saboda Gwamnati ta ce a dole ki karɓa. A wannan yanayi, maganar Gwamnatin nan kika yiwa biyayya amma ba kin karɓi wani abu mai daraja a hannuna ba. Idan na sayi kaya na ba ki kuɗi tamkar na isar miki da saƙon Gwamnati ne cewa
“Gwamnati ta ce ki ba ni kayan” sai na ba ki takardun kuɗi domin ki tabbatar saƙon daga Gwamnati ne ba ƙarya na ke ba. Takardun kuɗi suna a matsayin shaidar da mai kaya zai tabbatar daga Gwamnati su ke kuma ga darajar kayan da Gwamnati ta ce ki ba ni nan a rubuce a cikin takardun.
Amma idan muka waiwayi tarihin kuɗi za mu ga mutanen baya sun yi amfani da wasu abubuwa masu daraja ne wanda a karan kansu abubuwan suna da darajar da za a iya amfani da su a sarrafa wani abu kamar; zinare, gishiri, fata, azurfa da dai sauransu, dukkanin su za a iya amfani da su a sarrafa wani abun na amfani. Idan an karɓe su an bayarda kaya, to an karɓi abu mai daraja ne aka bayar da abu mai daraja. Saɓanin kuɗaɗen takarda ko na digital da mu ke amfani da su da ba su da wata daraja domin babu abin da za ka iya sarrafawa da su, kawai kana karɓa ne a matsayin dole.
Masana na kallon samuwar kuɗin fiat a matsayin wani ci gaba ta fuskar sauƙin sha’ani, amma kuma sun bautar da al’umma sakamakon tsirarun mutane ne su ke da ikon samar da su da ikon sarrafa su. Yau ko nawa gare ki sai Gwamnati ta so kiyi amfani da su sannan za ki iya amfani da su, idan ta so sai ta hana ki amfani da su, sannan idan ta so sai ta hana amfani da su ta kawo wanda ta ga dama. Saɓanin zamanin da a ke amfani da wasu abubuwan kamar zinare a matsayin kuɗi, kana da ikon sarrafa
kuɗaɗenka yadda ka ke so, idan ka so ma sai ka narka zinarin ka ƙera wani abun mai daraja da shi. Gwamnati ba ta da ikon cewa a daina karɓar su saboda suna amfani da yardar al’umma ne gaba ɗaya ba yardar Gwamnati kaɗai ba. Amma yau idan Gwamnati ta ce ta soke amfani da kuɗaɗen da mu ke amfani da su ta bugo sabbi to fa tsoffin sai dai su zamar maka shara, domin babu abin da za ka iya amfani da su ka
sarrafa, don haka masana su ke ganin suna da rauni ta fuskar inganci da kuma ƴanci.
Characteristics Of Money
Akwai siffofi da ɗabi’un nagarta da ya kamata duk wani abu da a ke
amfani da shi a matsayin kuɗi ya kasance yana da su. Mafi yawan abubuwan da mutane suka dinga amfani da su a matsayin kuɗi ba su gama cika ingantattu ba, saboda ba su gama haɗa dukkanin siffofin ba.
Kuɗi mai cikakken inganci shi ne wanda ya haɗa halayen nan guda shida:
1. Durable
2. Divisible
3. Transportable
4. Non-counterfeitable
5. Valuable
6. Generally accepted
Durable
Duk abin da za a yi amfani da shi a matsayin kuɗi ya kyautu abin ya kasance yana da; ƙarkon jimawa ta yadda za a iya adana shi na tsawon lokaci ba tare da ya lalace ba, komai tsawon lokacin da a ke amfani da
shi ba zai koɗe ba, kalar jikinsa ba za ta canja ba, idan fari ne zai tabbata
a matsayin farin ba zai koma wata kalar ba, idan an ajiye shi komai tsawon lokaci girman jikinsa da kaurinsa ba zai ragu ba, sannan yanayin zafi ko yanayin sanyi ba za su sanya ya ruɓe ko ya lalace ba. Bisa la’akari da haka za mu iya ganin da yawa daga cikin nau’ikan kuɗaɗen da al’umma daban-daban suka yi amfani da su ba kowanne ne
ya ke da ƙarkon da a ke buƙata ba, hatta kuɗaɗenmu na takardu ba su da ƙarkon jimawa sosai, saboda suna iya lalacewa ko su koɗe ko kuma su yayyage ya kasance sun yi lalacewar da ba za a karɓa ba sai dai a ƙona.
Bai kamata kuma a ce kuɗaɗe za su iya lalacewa ta yadda mai su zai yi asara ba, kamata ya yi nagartarsu ta tabbata yadda mai su ba zai yi asara don ya ajiye su na tsawon lokaci ba. Amma zinare a matsayin kuɗi idan muka duba za mu ga yana da ƙarkon da a ke buƙata; kalarsa ba ta koɗewa, adadinsa ba ya raguwa, ba ya
lalacewa ballantana wanda ke da shi ya zam ya yi asara, komai tsawon shekaru idan ka ajiye shi za ka same shi yana nan yadda ka ajiye shi. Haka su ma kuɗaɗen digital kasancewar su lambobi to su ma ba sa
lalacewa kuma ba sa koɗewa ko raguwa. Sai dai su kuɗaɗen digital da ya ke su nau’in kuɗin fiat ne da Gwamnati ke samarwa, ƙarkonsu ya ta’allaƙa ne da Gwamnati domin duk da ba sa lalacewa amma idan Gwamnati ta ce a daina karɓar su to sun tashi a matsayin kuɗi sun zama lambobin da ba su da bambanci da lambobin cikin calculator.
Divisible
Hali na biyu da ya kamata kuɗaɗe su kasance suna da su: su zama masu
sauƙin rarrabawa ta yadda za a iya amfani da su a sayi manyan kayayyaki da ƙananun kayayyaki. Amma idan ya kasance ba za a iya amfani da su a sayi ƙananun abubuwa ba sai dai manya, to ba su gama cika siffofin da za a iya kiransu da kuɗaɗe ingantattu ba.
A wannan fannin idan muka duba za mu ga abubuwa da yawa da aka yi amfani da su a matsayin kuɗi kamar; gishiri, sulallan zinare, kuɗaɗen takarda dama kuɗaɗen lambobi, dukkaninsu ana iya amfani da su a sayi
manyan kayayyaki har ma da ƙananu.
Transportable
Kafin kuɗaɗe su gama cika ingantattu, dole sai idan ana iya ɗaukar su a yi tafiya da su daga wani guri zuwa wani guri ba tare da an sha wahala sosai ba. Amma idan ya kasance kuɗaɗe ba za ka iya ɗaukar su ta daɗi ka tafi da su kasuwa ka yi sayayya ba, to suna da rauni ta fuskar inganci. A wannan ma idan muka duba za mu ga abubuwa da yawa da aka yi amfani da su a matsayin kuɗi yawancin su ana iya ɗaukar su ayi zirga- zirga da su ta daɗi, sai dai wasu sun fi wasu sauƙin zirga-zirgar.
Misali, kuɗaɗen zinare sun fi gishiri, fata da makamai sauƙin ɗauka a yi zirga-zirga da su, yayin da su kuma kuɗaɗen takarda sun fi na zinare sauƙin ɗauka da zagayawa duk inda a ke so, kuɗaɗen digital na lambobi
kuma sun fi kuɗaɗen takarda sauƙin ɗauka domin a cikin wayarka sai ka ɗauki adadin kuɗaɗen da sai an cika babbar mota da kuɗaɗen takarda ba a iya ɗaukeba.
Non-counterfeitable
Kafin kuɗi ya zama mai nagarta sai idan yana da wahalar kwaikwaya ta yadda mutane ba za su iya yin jabun su ba, saboda idan ya kasance kuɗaɗe suna da sauƙin bugawa to zai zama ba su da daraja ta yadda mutane da yawa za su zaɓi su buga kuɗin maimakon sarrafa kayan da
za su sayar su samu kuɗin. A wannan ma idan mu ka duba za mu ga; gishiri, fata, tagulla, tasa da zinare dukkanin su suna da wahalar kwaikwaya ko ma ba za a iya
kwaikwayon su ba. Su ma kuɗaɗen takarda suna da wahalar kwaikwaya sakamakon Gwamnati ta keɓe nau’in takarda da tawadar zana su ta yadda za su yi wahalar mallaka ballantana a buga kuɗi da su, duk da a kan samu lokuta da yawa wasu su iya buga jabunsu kuma ya zamanto mutane suna kashe su ba tare da sun iya bambanta jabun da na ainihi ba. Su ma kuɗaɗen digital a nasu ɓangaren suna da wahalar kwaikwaya sakamakon ikon samar da su yana hannun Gwamnati ne ita kaɗai.
Valuable
Masana suka ƙara da cewa, kuɗaɗe ba sa zama cikakkun ingantattu idan ba su zama suna da daraja a karan-kansu ba. Duk abin da da za a yi amfani da shi a matsayin kuɗi ya dace ya zamto yana da ƙima ta yadda
ko da an daina amfani da shi masu shi ba za su yi asara ba, domin za su iya amfani da shi su sarrafa kayan biyan buƙata da za su iya sayarwa a ba su kalar kuɗin da aka koma ana amfani da su. Amma idan ya kasance
kuɗaɗe ba su da wata daraja a karan kansu ta yadda idan aka daina amfani da su mai su ba zai iya sarrafa su ba sai dai ya watsar to ba su gama cika masu inganci ba.
A wannan fannin ma idan muka duba za mu ga yawancin abubuwan da aka yi amfani da su a matsayin kuɗi suna da amfani don ko da ma ba aba su matsayin kuɗi ba mutune na amfani da su kamar; gishiri, ƙarafuna,
makamai, fata da zinare. Amma kuɗaɗen takarda da kuɗaɗen digital dukkanin su ba su da wata daraja ko amfani, idan aka daina amfani da su ita kanta Gwamnati ƙona su ta ke yi saboda rashin amfanin su.
Darajar kuɗaɗen takarda da na digital daraja ce ta doka, Gwamnati ta zartar cewa a dinga karɓar su saboda haka mutane su ke karɓar su ba don suna da wata daraja ba. Sai dai wasu daga cikin masana kuma suna ganin duk da kuɗaɗen Gwamnati ba su da wani amfani ko daraja a karan kansu, amma wahalar kwaikwaya da su ke da su shi ma daraja ne, don idan ya kasance ba za ka iya samar da abu ba kuma kana buƙatarsa, idan kana son mallakarsa
sai ka yi aiki tuƙuru kafin ka samu, to iya wannan ma daraja ne. Koma dai ya ya, suna da darajar ne saboda Gwamnati ta zartar da dokar a ke ƙarbar su, idan gobe ta ce a daina amfani da su to sun zama abin da
Hausawa ke kira da “Fasassar ƙota ba ta moriya sai jifa.”
Generally Accepted
Abu na ƙarshe kuma mai mahimmanci da ya kamata kowanne kuɗi ya zama yana da shi, shi ne ya zama ilahirin al’umma suna karɓar sa a matsayin kuɗi. Amma idan ya kasance kuɗi ba a ko ina za ka je ka ba da su a karɓa ba, to ba su gama zama masu inganci ba.
A wannan fannin ma idan muka duba za mu ga abubuwa da yawa da aka yi amfani da su a matsayin kuɗi a zamaninsu ana karɓar su a kusan ko a ina, kamar zinare da a zamanin da a ke amfani da shi a matsayin kuɗi
babu yankin da za ka je ka ba da shi ba a karɓa ba, saɓanin kuɗaɗen Gwamnati wanda a ke karɓa a iya ƙasar da a ke sarrafa su kaɗai. Duk da ya ke kamar Naira duk inda ka je a faɗin Nijeriya ka miƙa ta za a karɓa a ba ka abin da ka ke buƙata, amma a wasu ƙasashen ba za a karɓa ba.
Dalilin da ya sa a ke iya karɓar zinare a ko ina cikin faɗin duniya azamanin da a ke amfani da shi a matsayin kuɗi shi ne, saboda al’umma
ne suka haɗu wajen yarda da shi a matsayin kuɗinsu ba ƙaƙaba masu shi aka yi ba, sannan kowa na iya haƙo shi gwargwadon adadin da zai iya, ba kamar kuɗin Gwamnati da ita kaɗai ce ke da ikon samarwa ba.
Centralization Vs Decentralization
Kuɗaɗen da al’umma su ke amfani da su tun daga ƙarnin baya har zuwa yanzu, samar da su da gudanar da su na faruwa ne a ƙarƙashin tsaruka guda biyu, watau centralization da decentralization.
Centralization: Wannan tsari ne na ba wa Gwamnati ko wata cibiya cikakken ikon sarrafa kuɗi da samar da kuɗaɗen a ƙarƙashin ikon cibiyar ko Gwamnatin ita kaɗai. Kuɗaɗen fiat da digital money da mu ke amfani da su dukkanin suna kan tsarin centralization ne, ikon sarrafa kuɗi da zaɓar abin da al’umma za su yi amfani da shi a matsayin kuɗi baya hannun al’ummar, maimakon haka yana hannun Gwamnati da
cibiyoyin kuɗaɗe.
Decentralization: wannan tsari ne na baiwa ilahirin al’umma damar samar da kuɗaɗe, adana su da gudanar da su. A wannan tsarin mutane za su iya haɗuwa su zaɓawa kansu abin da su ke so su yi amfani da shi a
matsayin kuɗinsu. Sannan kamfanoni da cibiyoyin da ba na Gwamnati ba suna da ikon samar da wani abu da za a dinga amfani da shi a matsayin kuɗi matuƙar dai al’umma suka yarda kuma suka amince da
abin to ya zama kuɗi. A ƙarƙashin wannan tsarin mutanen zamanin baya suka yi amfani da gishiri, fata, tasa, azurfa da zinare a matsayin kuɗi.
A tsarin ‘centralization’ za mu iya ganin yadda kuɗi suka dinga canjawa a ƙoƙarin al’umma na samar da kuɗaɗen da suka fi sauƙin sha’ani. Kuɗaɗe sun canja daga sulalla sun koma takarda daga nan suka komalambobi. Fifiko da alfanun amfani da kuɗaɗen digital ba zai misultu ba domin ta kowanne ɓangare kuɗaɗen digital sun fi na takarda inganci. To sai dai su kansunkuɗaɗen digital ɗin suna da rauni sakamakon Gwamnati kaɗai ce ke da iko akansu.
A ɓangaren ‘decentralization’ ma za mu ga yadda kuɗaɗe suka dinga canjawa daga wani abu zuwa wani abun har aka zo zamani amfani da zinare. Idan muka yi la’akari da halayen nan guda shida da kowanne kuɗi mai cikakkiyar nagarta ya ke da su za mu ga babu abin da ya fi zinare zama ingantaccen kuɗi domin yana da kusan duka halayen, a inda ya ke da rauni kawai bai wuce a ɓangaren ‘Transportable’ ba. Duk da ya ke zinare na da sauƙin zirga-zirga idan aka kwatanta da gishiri, amma ba za a iya kwatanta shi da kuɗaɗen takarda ko kuɗin digital wajen sauƙin ɗauka ba. Wannan dalilin ya sa masana suka ga akwai buƙatar samar da kuɗaɗen digital masu nagarta da hawa tsarin decentralization kamar zinare. Daga wannan ƙudirin ne aka samar da cryptocurrencies a matsayin kuɗaɗen digital masu kama da zinare ta fuskar inganci da kuma ƴanci. Hakan na nufin tsarin da aka fara amfani da shi na
decentralization an sake dawo da tsarin sannan aka zamantar da shi ta hanyar samar da kuɗaɗen digital da za su hau kan shi.
inshaAllahu darasin mu na gaba zai zama sharar fage akan crypto currency, wato:
INTRODUCTION TO CRYPTOCURRENCY

Leave a comment