Tsari da kuma dokokin gabatar da shirye shiryen mu.


Yana da kyau kowace admin, moderator da kuma masu gabatar da shirye shirye su karanta wadannan ka’idoji da tsarukan daya kamata su bi kuma su kiyaye a yayin gudanar da shirye shirye. Domin sabawa wadannan dokoki ka iya jawo fushin doka akan mutum.

1. APPROVE NA POST: Kowace rana daga 9am zuwa 11:30am (Lokacin shirin safe) da kuma 5pm zuwa 9pm (Lokacin shirin yamma) ba’a yarda kowace admin tayi approve na post ba matukar ba itace take jagorancin shirin da yake wakana a daidai wannan lokacin ba, sannan kuma idan wata tayi miki approve na post a lokacin gabatar da shirinki wajibi ne ki gaggauta shigar da korafi zuwa ga kwamitin ladaftarwa idan kuma bakiyi haka ba har su kwamitin suka gano da kansu to fa kema zaki fuskanci hukunci. Ranar Juma’a gaba daya babu approve na post sai idan kina cikin masu gabatar da shirin “Addininmu Alkiblarmu”.

2. Duk wadda zata gabatar da shiri yana da kyau ta shirya tun kafin zuwan ranar ko lokacin da zata gabatar da shirin. Zaki iya amfani da Notes na wayarki ko WPS ki shirya rubutunki kuma ki tabbatar kinbi rubutunki sannu a hankali domin gyara kura kuran da zaki iya yi.

3. Bamu yarda da gajarta rubutu ba a yayin gabatar da shirye shiryen mu, duk abinda zaki rubuta ki rubuta shi da cikakkun harufansa.

4. Idan an hadaku da abokiyar aiki yana da kyau idan kun tsara abinda zaku gabatar ku tuntubi junanku kafin ku fara gabatar da shiri, sannan kuma idan wani uzuri ba zai bari ki samu damar gabatar da shirin ba ki tabbatar kin sanar da abokiyar aikinki akan lokaci.

InshaAllahu zuwa yamma zanyi rubutu akan yadda kowabe shiri ya dace a gabatar dashi domin taimaka mana wajen kara fahimtar aikin dake gabanmu

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started