MATA MU DAWO HAYYACINKU


Wallahi al’amarin yan uwana mata yana matukar bani takaici, kowa kawai kanta ta sani, a wannan zamanin maganar ciwon ya mace na ya mace ne kwata kwata bata tasiri a tsakaninmu.
Kullum muna maganar hadin kai, zumunci da taimakon juna amma babu wani kokari da muke yi wajen tabbatar da hakan a aikace, domin wallahi hadin kai da kaunar juna bata taba samuwa dole sai da sadaukarwa.
Saboda tsabagen rashin kishin kai da muke fama dashi yar uwarki mace tana cikin mawuyacin hali amma ba zaki iya sadaukar da komai kankantar abinda kike dashi wajen ganin kin taimaka mata ba, to meye amfanin taruwar tamu a cikin group kawai dama dan muzo muyi ta bata lokacinmu a banza ne sam ba haka bane kuma ba shine dalilin bude wwnnan group ba kuma ba zamu lamunci hakan ba.
Ina magane ne akan abubuwa guda biyu da nayi posting kwana biyu zuwa uku da suka wuce kuma wanda yafi bata min rai ma shine na baiwar Allah da nace a yan garin tsafe su bincika min asibitin Dr. Bawa ance anan aka kwantar da ita amma mirsisi, bafa cewa akayi wata ta taimaketa da sisin kobo ba, a’a ni zanyi amma a rasa wadda zata sadaukar da 30mins zuwa 1h tayi taimakon da ta dalilin haka sai Allah ya bata Aljanna kuma abin takaicin ma yar uwarki mace za’a taimakawa.
Na biyu maganar baiwar Allah data haihu a cikin yanayin jarabawa wanda ba wanda yafi karfin Allah ya jarrabeshi sama da irin wadda yayi mata amma mutane sukayi mirsisi, alal akalla yau ace a cikin mutane sama da dubu uku da suke gidan nan a samu mutum 100 koda 500 ko wanne ya bada an samu 50k zaiyi matukar taimaka mata wajen hidimar suna kuma ba zata taba mantawa da mutanen gidan nan ba sannan na tabatar idan yau wata matsala ta samu daya daga cikinmu zata taimaka sai inda karfinta ya kare.
Gaskiya mu chanja tunani mafi karanci 200 da yawanmu 200 ko data bazata saya mana ba, Muyi amfani da hankalinmu mana, yau wata ta nemi taimako nayi scrolling na wuce anya ban yaudari kaina ba idan nayi tunanin wata rana idan na nemi taimako ba haka za’ayi ta scrolling ana wucewa ba, ko kuwa ina da guarantee akan yadda rayuwa zata kasance min nan gaba, tunda suma wadanda suke neman taimakon mostly ba a haka suka fara rayuwa ba, kuma koma a haka suka fara babu wanda yasan me zasu zama nan gaba.
Ina fada muku wannan ne saboda na taba shiga yanayi na neman taimako makamancin wannan a rayuwata ta baya a gaban idona dan uwana yabar duniya akan mun kasa biya masa 5.8m domin yi masa surgery kuma ba irin posting din da ba’ayi ba a Facebook a wancan lokacin. Abin takaicin shine zaka samu group na facebook bila adadin masu members 300k 500k ko sama da haka ma kuma hausawa sannan musulmai amma hakan bai yi mana amfanin komai ba, ko kunsan a wancan lokacin a cikin group mai mutum 500k idan 200k kowa zai bayar da naira talatin kawai sai an hada wancan kudin harda sauran 200k, idan a wancan lokacin wani group ya samar mana koda 1m ne har duniya ta tashi kuna tunanin zan manta da group din? yanzu na tabbatar a cikin wadanda suke da halin da zasu iya bada gudummawar 1000 a wancan lokacin yanzu dayawansu suna bukatar taimako ko basa neman taimako na tabbatar yanzu dayawa daga cikinsu na fisu karfi kuna tunanin zanga post na neman taimako a wancan group din banyi wani abu a kai ba..
Ni nazo kawo chanji ne akan waccan matsalar kuma na shirya fuskantar kowane kalubalai dan ganin chanjin ya tabbta.
InshaAllahu nan bada jimawa ba zamu zabi mutum uku wanda zasu rike mana TREASURY na group din nan kuma zamu bude musu account kawai domin magancewa yan uwa mata matsalolinsu wadanda suke bukatar kudi, Admins lallai ku tuna min idan munzo meeting.
Admins wajibine ku bada taku gudummawar, Ina so naga gudummawar kowace admin, idan members hadin kan ba zai samu a tsakanin members ba mu wajibi ne mu samar dashi a tsakanin mu.
A karshe ina sanar da cewa har yanzu kofa a bude take, daga nan zuwa Friday InshaAllahu zamu sanar da abinda aka samu sannan mu duba iyuwar damka mata su a hannunta ko yi mata sayayyar da ake bukata.
Account Number: 8060960906
Account Name: Rukayya Haruna Ibrahim
Bank Name: Opay/paycom

MATA MU DAWO HAYYACINKU

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started